Harin 'yan bindiga: Zulum ya ba wa mutanen Zamfara tallafin naira miliyan 20
- Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya kai ziyarar jaje Jihar Zamfara a madadin gwamnonin yankin arewa maso gabas
- Yayin ziyarar, Zulum ya bada tallafin naira miliyan 20 ga al'ummar da hare-haren yan bindigan na baya-bayan nan ya shafa a Zamfara
- Kazalika, Zulum yayin jawabinsa ya karfafa wa Zamfarawa gwiwa inda ya ce kada su karaya domin shi kansa Boko Haram sun masa barna a jiharsa
Jihar Zamfara - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara Jihar Zamfara domin jajantawa mutanen jihar game da hare-haren da yan bindiga suka kai musu a baya-bayan nan a madadin gwamnonin arewa maso gabas.
Zulum, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin na arewa maso gabas, ya ziyarci fadar gwamnan Jihar Zamfara da ke Gusau ne a ranar Litinin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
A lokacin da ya kai ziyarar, Zulum ya bada tallafin naira miliyan 20 ga mutanen da hare-haren yan bindigan ya shafa.
Cikin wadanda suka yi wa gwamnan rakiya zuwa Gusau, akwai Sanata Ali Ndume, Shugaban Kwamitin Sojan Kasa a Majalisar Dattawa, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Borno Abdullahi Musa Askira.
Zulum ya karfafa wa Zamfarawa gwiwa a yayin jawabin da ya yi wa sarakunan gargajiya da jami'an gwamnatin Zamfara, inda ya ambaci irin barnar da Boko Haram ta janyo a jiharsa ta Borno.
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani rahoton, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Ya ce:
"Muna kara matsowa shekarar 2023 inda za a yi babban zabe, amma a wuri na bai da wani muhimmanci. Ba na fatan neman wata kujera. Ban taba fatan zan zama gwamnan Jihar Borno ba ma kuma bana fatan sake neman wata kujerar da ta fi ta amma a matsayin na na musulmi, ina addu'ar abin da ya fi alheri."
Asali: Legit.ng