Yan Arewa 104,403, yan kudu 23,088 suka nemi aikin yan sanda, ga jerinsu
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta sanar da fara tantance daukar sabbin jami'ar ta 2021 da za'a dauka 10,000.
A cewar hukumar, mutane 127,491 ne suka cike fom din shiga aikin ‘yan sanda.
Zasu je ranar Talata 1 ga watan Fabrairu a hedikwatar ‘yan sanda ta jihohi a fadin kasar domin a duba lafiyarsu.
Manyan yan kudu sun koka kan yadda yan yankin suka ki neman aikin gaba daya.
Kakakin yan sanda, Frank Mba, ya ce sai da hukumar ta dage rijistan saboda a baiwa yan kudu daman rijista.
A jawabin da ya saki makonni biyu da suka gabata, yace an yi haka ne don tabbatar da cewa an nuna daidaito tsakanin kudu da Arewa.
Ga jerin jihohi da adadin wadanda suka nema:
1. Jihohin Kudu
Abia state has 596
Akwa Ibom 3,536
Anambra 314
Bayelsa 759
Cross River 2,704
Delta 976
Ebonyi 463
Edo 1,206
Ekiti 1,417
Enugu 707
Imo 852
Lagos 562
Ogun 1,154
Ondo 2,472
Osun 2,006
Oyo 1,767
Rivers 1,597
2. Jihohin Arewa
Plateau 4,100
Kebbi 3,596
Katsina 7,605
Kano 7,557
Kaduna 7,436
Jigawa 4,951
Benue 6,578
Adamawa 8,206
Bauchi 7,140
Borno 8,693
Abuja 4,418
Kogi 4,412
Kwara 2,410
Nasarawa 4,700
Niger 4,672
Sokoto 2,450
Taraba 4,075
Yobe 4,992
Gombe, 4,416
Zamfara 1,990
Asali: Legit.ng