Hotunan jiga-jigan da suka dira masarautar Gaya naɗin sarautar sabon sarki

Hotunan jiga-jigan da suka dira masarautar Gaya naɗin sarautar sabon sarki

  • Hamshakai da jiga-jigan mutane daga sassan duniya sun yi tururuwa zuwa masarautar Gaya domin bikin nadin sarautar sabon Sarki
  • Gwamna Ganduje na jihar Kano ya mika sandar sarauta tare da gabatar da ma'aikata ga Sarki Aliyu Ibrahim Gaya wanda ya gaji marigayin mahaifin sa
  • Sarki Aliyu Ibrahim Gaya wanda ake kira da Kirmau Mai Gabas, ya bayyana murnar sa da godiya ga Ubangiji da ya bashi rai da lafiya har ya gaji sarautar magabatan sa

Gaya, Kano - Jiga-jigai daga sassan duniya, a ranar Asabar, sun hallara garin Gaya a Kano domin nadi da gabatar da ma'aikata ga Aliyu Ibrahim Gaya (Kirmau Mai Gabas) a matsayin sarki.

Sabon sarkin ya gaji marigayin mahaifin sa, Ibrahim Abdulkadir, wanda ya kwanta dama a 22 ga watan Satumba ya na mai shekaru 91, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya na gina tituna 21 a jihar Kano, Minista Fashola

Hotunan jiga-jigan da suka dira masarautar Gaya naɗin sarautar sabon sarki
Hotunan jiga-jigan da suka dira masarautar Gaya naɗin sarautar sabon sarki. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Nadin ya biyo baya ne bayan an gabatar wa masu nadin Sarki mutane Uku da suka cancanta inda daga ciki ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya zabi Aliyu Ibrahim Gaya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kafin zaben shi matsayin sarkin Gaya, Ibrahim ya rike sarautar gargajiya ta Ciroman Gaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban Limamin Gaya, Tijjani Jazuli Gaya, ya rantsar da sarkin wanda yayi rantsuwa da zama shugaba na kwarai kuma abin koyi sannan uba ga mutanen kwarai a masarautar Gaya.

Yayin taya murna ga sabon Sarkin, Sarkin Musulmai, Sa'ad Abubakar ll, ya yi kira kan zaman lafiya tare da addu'a ta musamman ga shuwagabanni da kasa baki daya.

Ya yi wa sabon sarkin fata nagari gami da sa ran zai zamo jagora na kwarai yadda marigayin mahaifin sa ya rayu a kan nagarta irin koyarwar addinin Islama.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

A bangaren Gwamna Ganduje, yayi jan kunne ga sarkin da kada ya bari martabar masarautar ta yi kasa kuma ya manta da duk wani abu da zai janyo tabarbarewar sarautar gargajiyar.

Ya bada tabbacin cewa, gwamnatin sa a shirye ta ke ta taimaka ga duk abin da zai kara habaka darajar masarautar.

Sarkin ya nuna godiya ga Ubangiji da ya ba sa rai da kuma damar hawa karagar mulkin.

Ya kara da godiya ga Gwamnatin Jihar Kano da mutanen kwarai na masarautar Gaya da suka ga ya cancanta ya gaji karagar.

A saboda haka ne ya ke kira ga mutanen kwarai na masarautar Gaya da su cigaba da taimaka masa don ganin ya gudanar da mulkin sa yadda ya dace.

Masarautar Gaya ta na daya daga cikin masarautun da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya samar a 2019.

Ita ce guri mafi dadewa kuma muhimmiya a tarihin Kano kuma guri mafi daraja a masarautar Kano.

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

Gaya ita ce asalin mutumin nan mai suna Kano wanda ya fara zama a jihar Kano dalilin neman lu'u- lu'u.

Wadanda suka fara zama Kano su ne ake wa lakabi da "Abagayawa". Gaya ta taba zama masauki ga 'yan gudun hijara wacce ta zama matattarar mutanen da suke hijira musamman daga gabashin Sudan, yammaci da tsakiyar Gabas.

Sabuwar masarautar da aka kafa ita ce ta shafe sunan Gaya saboda tarin al'adu da sababbin shuwagabannin ta kuma za ta zama daya daga cikin birni mai fadi-a-aji a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel