Da duminsa: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, ya mutu

Da duminsa: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, ya mutu

Wani dan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltan mazabar Gusau 1, Ibrahim Na-Idda, ya rigamu gidan gaskiya.

Dan majalisar ya mutu ne da daren Juma'a a Asibiti FMC Gusau bayan doguwar rashin lafiya da yayi, rahoton TVC.

Dan majalisar ya mutu yana mai shekaru Sittin da bakwai (67).

Ibrahim Na-idda
Da duminsa: Dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Ibrahim Na-idda, ya mutu Hoto: TVCNewsNg
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dirakta Janar na yada labarai da hulda da jama'a na majalisar dokokin, Jafaru Kaura, ya bayyana hakan.

Tuni an yi jana'izarsa bisa koyarwan addinin Musulunci.

Marigayi Ibrahim Na-Idda ya bar mata hudu, 'yaya ashirin da shida da sauran yan'uwa.

Mutuwar Na-Idda na zuwa ne watanni shida bayan mutuwar Hon. Ibrahim Ahmad da ya wakilci mazabar Shinkafi.

Kara karanta wannan

Hotunan wasu ƴan kabilar Igbo yayin da suke karɓar shahada a masallacin Jihar Enugu

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng