Tashin Hankali: Tankar man fetur ta fashe ta kama da wuta a tsakiyar gidan mai

Tashin Hankali: Tankar man fetur ta fashe ta kama da wuta a tsakiyar gidan mai

  • Da safiyar Asabar ɗin nan, mazauna yankin Aba Road a babban birnin jihar Abia, sun tashi da wani mummunan lamari
  • Wata Tankar man fetur ta yi bindiga a tsakiyar gidan mai dake kan hanyar Aba, kuma rahoto yace gidan man na wani minista ne
  • Tuni dai mutane suka fara kokawar kashe wutar tare da jami'an hukumar kashe wuta na jihar Abia

Abia - Wata Tankar man futur ta yi bindiga ta kama da wuta a harabar wani gidan mai dake Umuahia, babban birnin jihar Abia, ranar Asabar da safe.

Daily Trust ta rahoto cewa Mazauna yankin Aba Road a babban birnin na Abia sun wayi gari hayaƙin wuta ya tunnuƙe Anguwarsu daga gidan mai.

Tankar Man Fetur ta fashe
Tashin Hankali: Tankar man fetur ta fashe ta kama da wuta a tsakiyar gidan mai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton da muka samu daga yankin ya nuna cewa gidan man da abun ya shafa mallakin wani minista ne dake kan kujera, amma ba'a faɗi sunan sa ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje a jihar Kano ya ɓace

Duk da babu wanda ya san musabbabin faruwar lamarin, amma wutar ta ci karen ta babu babbaka na tsawon awanni biyu ba tare da kokarin jami'an kashe gobara ya yi tasiri a kanta ba.

Gidan man da Tankar ta fashe ya na gab da gidajen mazauna babban birnin a kan hanyar Aba, kuma kilomita kaɗan tsakanisa da cibiyar birnin.

Mazauna yankin sun fito da bokitan ruwa yayin da suke taimaka wa jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Abia wajen shawo kan lamarin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Ɗan kwamishiniyar Ganguje a jihar Kano, Dakta Zahara'u, ya ɓace ba'a san inda yake ba

Rahoto daga Kano ya nuna cewa ɗan kwamishiniyar mata da walwalar al'ummar, Dakta Zahara'u Muhammad Umar, ya bata ba'a san inda yake ba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tanka makare da man fetur ta fashe ta kama da wuta, ta yi mummunan ɓarna a Onitsha

A ranar 17 ga watan Janairu, 2022, Abdurrahman Abdu Usman, ya bar gida da nufin komawa jihar Katsina wurin da yake aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC).

Tun bayan tafiyarsa, Abdurrahman, bai tuntuɓi gida ba kuma ko an nemi wayarsa ta hannu ba ta shiga, hakan ya ta da hankulan iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262