Jiga-jigan siyasa, yan kasuwa, attajirai sun dira auren 'dan Dahiru Mangal
- Dan Shahrarren Attajiri dan jihar Katsina, Alhaji Dahiru Barau Mangal, ya angwance da amaryarsa a Abuja
- Manyan yan siyasa sun hadu a unguwar Maitama don shaida daurin auren da Shugaban Izalah ya daura
Jiga-jigan siyasan All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Juma'a sun ajiye siyasa gefe yayinda suka halarci taron daurin auren dan attajiri, Alhaji Dahiru Mangal.
An daura auren Shamsudeen Mangal, da Habeeba Ayuba Musa a Masallacin Abi Talib dake unguwar Maitama, birnin tarayya Abuja, rahoton DailyTrust.
Daga cikin wadanda suka hallara akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Sauran sune Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; da Shugaban majalisa na yanzu, Ahmad Lawan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan jihar Katsina wanda shi yayi wakilin Ango ya biya kudin sadaki N500,000.
Sheikh Abdullahi Bala Lau, wanda ya daura auren ya bayyana muhimmanci da manufofin daurin aure a addinin Musulunci.
A cewarsa, daya daga cikin manufofin aure shine karfafa zumunci tsakanin 'yan uwa da abokan arziki.
Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa
Allah ya yiwa Hajiya Murja Mangal, mahaifiyar shahrarren attajiri dan jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.
Hajiya Murja ta mutu ne a daren Alhamis tana mai shekaru tamanin da biyar (85) bayan gajeruwar jinya.
An za'a gudanar da jana'izah bayan Sallar ranar Juma'a 21 ga watan Junairu, 2022.
Asali: Legit.ng