Na kasa daina sata: Matar da ta fara sata tun tana shekaru 7 ta ba da tarihin rayuwarta

Na kasa daina sata: Matar da ta fara sata tun tana shekaru 7 ta ba da tarihin rayuwarta

  • Wata ‘yar kasar Ghana ta bayyana yadda ta ke fama da matsalar son daina sata a wata hira da ta yi da gidan talabijin na Crime Check TV GH
  • Ta bayyana cewa munanan dabi’arta ta fara ne tun tana shekara bakwai a lokacin da mahaifinta da ya haifi ‘ya’ya da dama da mata daban-daban ya gaza kula da ita
  • Matar ta bayyana cewa ta taba shiga gidan yari har sau hudu kuma hakan ya faru ne saboda ta gagara daina sata

Wata ‘yar mata 'yar Ghana mai shekaru 30 da haifuwa an yi hira da ita a wata tashar YouTube mai suna Crime Check TV GH inda ta bayyana irin dabi'arta ta satar da take fama dashi.

Bidiyon da Legit.ng ta gano ya ba da labarin yadda matar ta fara sata tun tana karama kuma har hakan ya kai ta ga shiga gidan yari har sau hudu saboda tsabar sata.

Kara karanta wannan

Yarinyar kirki: Mai tallan 'Pure Water' ta tsinci kudade, ta kai cigiya gidan radiyo

Mata mai yawan sata ta bayyana yadda ta fara tun tana shekara 7
Na gagara daina sata: Matar da ta fara sata tun tun tana karama ta ba da labarinta mai ban tausayi | Hoto: Crime Check TV GH/YouTube
Asali: UGC

Yadda ta fara sata

Matar da a yanzu ta nuna nadama ta ba da labarin cewa mahaifinta yana da ‘ya’ya da mata da dama kuma bai damu da yaransa ba don haka ta koma sata don ta biya wa kanta bukata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin faifan bidiyon, ta bayyana cewa karon farko da ta shiga gidan yari shine lokacin da ta saci kaya kuma aka yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu ne.

Ta ci gaba da cewa bayan an sake ta, rayuwa ta yi mata matukar kunci, don haka ta yanke shawarar sake tafka wata satar kuma a nan ma aka sake kama ta.

Matar mai da daya ta bayyana cewa ta saci gashin kanti guda biyar a wani shago kuma anan aka kama ta aka yanke mata hukuncin watanni 9 a magarkama.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa mahaifi ɗaurin rai-da-rai saboda ɗirka wa ƴar cikinsa ciki

Tana son canza halinta

Matar ta kuma ba da labarin cewa tana ta fafutukar yadda za ta daina sha'awar abubuwan da ba nata ba.

Ta kuma bayyana cewa a wasu lokuta abubuwan da take sacewa ba su da wata ma'ana amma ba za ta iya gani ta bari ba.

Matar mai shekaru 30 ta ba da cikakken bayani kan yawan satar da tayi a cikin bidiyon da muka samo a kasa:

A bangare guda kuwa, wata mai tallan ruwan leda ta ja hankalin ‘yan Najeriya bayan da ta mayar da wasu kudade da ta tsinta a lokacin da ta ke talla a jihar Gombe.

Yarinyar mai suna Zainab ta tsinci N12,000, wasu daloli da Yen na kasar Japan. Sai dai a maimakon ta dauki kudin ta kashe, an ce ta yi gaggawar kai rahoton lamarin ga wani gidan rediyo. Ta nemi a yi cigiya domin a gano mai shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki

Hoton kudaden da Legit.ng ta gani ya nuna cewa kudin masu daraja daban-daban ne da suka hada da N500 da N1000, Yen na Japan, da kuma takardar Dala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: