Yarinyar kirki: Mai tallan 'Pure Water' ta tsinci kudade, ta kai cigiya gidan radiyo

Yarinyar kirki: Mai tallan 'Pure Water' ta tsinci kudade, ta kai cigiya gidan radiyo

  • Wata yarinya mai talla ta bai wa ‘yan Najeriya da dama mamaki bisa yadda ta nuna tsantsar gaskiya a jihar Gombe
  • Yarinyar mai suna Zainab ta tsinci dala, Yen na Japan da kuma N12,000, amma ba tare da bata lokaci ba ta kai cigiya ga wani gidan rediyo inda ta nemi mai kudin
  • ‘Yan Najeriya da dama na yabawa yarinyar da ke tallan ruwa saboda nuna tsantsar gaskiya da kiyaye kai daga abin da ba nata ba

Wata mai tallan ruwan leda ta ja hankalin ‘yan Najeriya bayan da ta mayar da wasu kudade da ta tsinta a lokacin da ta ke talla a jihar Gombe. Yarinyar mai suna Zainab ta tsinci N12,000, wasu daloli da Yen na kasar Japan.

Sai dai a maimakon ta dauki kudin ta kashe, an ce ta yi gaggawar kai rahoton lamarin ga wani gidan rediyo. Ta nemi a yi cigiya domin a gano mai shi.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Zainab mai gaskiya
Yarinyar kirki: Mai tallan fiya-wata ta tsinci kudade, ta kai cigiya gidan radiyo | Hoto: @ijeomadaisy
Asali: Instagram

Hoton kudaden da Legit.ng ta gani ya nuna cewa kudin masu daraja daban-daban ne da suka hada da N500 da N1000, Yen na Japan, da kuma takardar Dala.

'Yan Najeriya sun yabawa Zainab kan gaskiyarta

'Yan Najeriya da suka ga labarin a lokacin da @ijeodaisy ya wallafa a shafin Instagram, sun yi ta yabawa yarinyar kan yadda ta mai da kudin. Ga kadan daga cikin abubuwan da suke cewa:

@iamjulieuche ya ce:

"Wannan yarinya ce da ta fahimci tarbiyar da iyayenta suka ba ta."

@yes_iam_chi_dalu ya rubuta:

"Ina addu'ar wani ya ga wannan kuma ya canza rayuwarta da kyau."

@dndluxury_ yayi sharhi:

"Awwwww ina addu'a Allah ya saka mata da wannan aikin na alkhairi, wannan ya kamata ya zama abin koyi ga tsararrakinta, Allah ya mata albarka."

Kara karanta wannan

Masu jini muke so: Gwamna ya caccaki tsofaffin da ke kwalamar kujerar Buhari

@louislatush ne ya rubuta

"Lol masu gaskiya a cikin kasar marar gaskiya."

Kalli hotonta:

Shekaru 18 basu kwana a kan gado ba saboda talauci, an canza rayuwarsu

A baya kunji cewa, wasu ma'aurata a garin Kandara da ke Murang'a na kasar Kenya na cikin farin ciki bayan da masu hannu da shuni suka kawo musu dauki bayan shafe shekaru suna rayuwa cikin kunci tare da 'ya'yansu.

Peter Waweru, wanda ya kwashe shekaru da yawa baya iya motsawa bayan fama da rashin lafiya, yana zaune ne tare da iyalansa a wani gidan da ke daf da rugujewa.

An yi sa'a, wasu mutanen kirki karkashin jagorancin mawakiyar Kikuyu, Anne Lawrence, sun tausaya musu ganin irin mawuyacin halin da suke ciki, inda suka fara fafutukar ginawa Waweru da iyalinsa gida mai mai har ma da bandakinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: