Gwamnonin Najeriya na zargin NNPC da laifin sata da noke gaskiya a kan batun man fetur
- Kungiyar gwamnonin jihohi ta zauna da shugabannin ‘yan kasuwa da ‘yan kwadagon Najeriya
- A wannan taro, shugaban NGF watau Kayode Fayemi ya nuna rashin yardarsu da kamfanin NNPC
- Gwamna Kayode Fayemi ya ce akwai bukatar 'Yan Najeriya su san gaskiyar lamarin tallafin man fetur
Abuja - Yayin da ake ta muhawara a kan batun cire tallafin man fetur a Najeriya, kungiyar gwamnonin jihohin tarayya ta NGF ta fito ta jefi NNPC da zargi.
Gwamnonin na Najeriya su na tuhumar kamfanin mai na kasa, National Petroleum Corporation Limited (NNPC) da laifin sata da kuma kin bayyana shirin na su.
A ranar Alhamis jaridar Premium Times ta rahoto kungiyar gwamnonin ta na cewa akwai noke-noke da boye gaskiyar lamarin tallafin man fetur da NNPC ke yi.
A ra’ayin NGF, babu wanda zai gamsu da cire tallafin fetur sai an san asalin abin da ke faruwa.
Gwamnonin sun bayyana wannan ne a wajen wani taro da suka yi da kungiyar NLC ta ‘yan kwadago da kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC a birnin tarayya Abuja.
Kan kungiyar gwamnonin jihohi da NGF da kuma NLC duk ya hadu a kan cewa hukumomi su na boyewa al’umma gaskiyar abin da ake ciki a game da tallafin mai.
A taron na ranar Laraba, an fito baro-baro ana zargin NNPC da facaka da kudin da kasa take samu.
Zargin da NGF ta ke yi
“Saboda akwai rashin gaskiya sosai a game da alkaluman man da kasar nan ta ke sha.”
"Za mu iya samun cigaba ne kawaii dan NLC ta zauna da wadanda suka san gaskiyar abin irinsu PENGASSAN domin ayi bincike kafin daukar wani mataki.”
“Kusan jihohi takwas kadai suke amfana kai-tsaye daga tallafin man fetur, yayin da sauran jihohin sai dai su yi hakuri da halin da suka samu kansu.” – NGF.
Zaman NGF da NLC da TUC
Rahoton ya ce kungiyar NGF tayi wannan ganawa da wakilan ‘yan kwadago da ‘yan kasuwan kasar ne a game da batun cire tallafin man fetur da ake sa rai za ayi.
An yi wannan taro ne jim kadan bayan an ji cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta dakatar da karin litar fetur. Sai dai nan gaba za a iya janye tallafin na man fetur.
Dama tun tuni an ji cewa Gwamnan jihar Ekiti ya shaidawa manema labarai NGF za ta tattauna da wakilan NLC da TUC kan yadda za a bullowa lamarin farashin mai.
Idan an janye tallafin fetur, dole litar mai zai tashi sosai wanda zai sa mutane su fito su koka.
Asali: Legit.ng