Kisan Hanifa: An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai
- Matar mutumin da ya kashe Hanifa Abubakar ta shiga hannun 'yan sanda, an kai ta kotu amma ta musanta zargin da ake mata
- Kotu ta tuhumi Jamila Muhammad Sani da laifuka hudu da ke da alaka da sacewa da kisan Hanifa Abubakar
- Kotu ta umarci a ajiye Jamila Muhammad Sani a magarkamar 'yan sanda har zuwa lokacin da za a warware komai
Kano - Jamila Muhammad Sani, matar makashin Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, ta gurfana a gaban babban kotun majistare na jihar Kano da ke zama a Gidan Murtala, Kano, bisa zargin hannu a boye Hanifa.
Jamila, ‘yar shekara 30, matar Abdulmalik Tanko ce, wanda ake shari’a kan tuhume-tuhume hudu da suka hada boye wacce aka yi garkuwa da ita, hada baki, garkuwa da dan mutum da kuma kisan kai.
Mai gabatar da kara, a yayin da take karantawa Jamila rahoton farko na bayanai, ta yi zargin cewa ta boye wacce aka sace a gidanta na tsawon kwanaki biyar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda aka gabatar da tuhumar farko kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ke Jamila Muhammad Sani, matar Abdulmalik Tanko Muhammad, mamallaki kuma malamin makarantar Noble Kids Comprehensive Academy dake Kwanar Dakata a jihar Kano, a ranar 4 ga Disamba 2021 da misalin karfe 18:30 mijinki ya kawo miki Hanifa Abubakar mai shekaru 5 sanye da kayan makarantarta kuma ta yi kwana biyar a hannun ku.
"Kin boye ta da sanin cewa mijinki ne ya sace ta kuma kin ki bayyanawa kowa."
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da sashe na 227 na kundin laifuffuka.
Jamila ta musanta abin da rahoton na farko ya kunsa.
Don haka, lauya mai shigar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya roki kotun da ta tasa keyar Jamila ga magarkamar ‘yan sanda har sai an kammala shari’ar.
Alkalin kotun Majistare Muhammmad Jibril ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Jamila a hannun ‘yan sanda sannan ya dage zaman zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Kano ya ce dole a tabbatar an yi adalci a lamarin, inda yace zai bukaci a kammala hukuncin cikin gajeren lokaci, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Gwamnan a baya ya ce zai amince da rattaba hannu kan hukuncin kisa ga Abdulmalik, mutumin da ya kashe Hanifa.
Makashin Hanifa ya bayyana a kotu, an dage shari'a zuwa wasu kwanaki
A wani labarin, Shugaban makarantar Noble Kids da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, Abdulmalik Tanko, ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kano.
An gurfanar da shi a gaban babban alkalin kotun, Muhammad Jibril, kan kisan gillar da ya yi wa Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar, wata dalibarsa da ya sace.
Abdulmalik ya amsa laifin kashe Hanifa da gubar bera bayan ya sace ta a watan Disamba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng