Karya ne jirgin mu be hatsari ba, Hukumar yan sanda ta bayyana gaskiyar abin da ya faru

Karya ne jirgin mu be hatsari ba, Hukumar yan sanda ta bayyana gaskiyar abin da ya faru

  • Hukumar yan sandan ƙasar nan ta musanta rahoton da ake yaɗa wa cewa jirgin ta ya yi hatsari a Bauchi har wasu mutane sun jikkata
  • Kakakin hukumar na ƙasa, Frank Mba, yace jirgin ya taso daga Abuja kuma ya isa Bauchi da safiyar Alhamis, ya sauka lafiya
  • Yace matsala ɗaya da ta faru shi ne yayin saukar jirgin wutsiyarsa ta daki wata bishiya, amma babu wanda ya ji ko kwarzane

Abuja - Hukumar yan sandan ƙasar nan ta musanta rahoton dake yawo cewa jirgin Helikwaftan yan sanda ya yi hatsari a Bauchi.

The Nation ta rahoto cewa wani jirgin Helikwafta na hukumar yan sanda ya yi hatsari a Bauchi, inda lamarin ya jikkata mutum shida ranar Laraba.

Da yake martani game da wannan lamarin, kakakin yan sanda na ƙasa, Frank Mba, ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa, jirgin ba hatsari ya yi ba.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Frank mba
Karya ne jirgin mu be hatsari ba, Hukumar yan sanda ta bayyana gaskiyar abin da ya faru Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Kazalika kakakin yan sanda ya yi bayanin cewa matukin jirgin mai saukar Angulu ya samu nasarar shawo kan jirgin ya sauka.

Mista Mba ya ƙara da cewa jirgin ya taso ne daga babban birnin tarayya Abuja, kuam ya dira a Bauchi da misalin ƙarfe 7:00 na safe, amma ya tarad da fitulun sauka a kashe.

Shin meyafaru da Helikwaftan?

A cewar mai magana da yawun yan sandan wutsiyar jirgin ce kawai ta ɗan samu matsala, amma matukin ya sauka lafiya.

Daily Trsut ta rahoto Frank Mba ya ce:

"Ba hatsari jirgin mu ya yi ba. Ya sauka lami lafiya a Bauchi. Jirgin ya tashi daga nan Abuja kuma ya isa Bauchi da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau Alhamis."
"Amma bisa rashin sa'a sai suka tarad da fitilun sauka a kashe, da farko sun tsaya cak a sama kusa da filin jirgi, suka yi kokarin kiran ma'aikata domin a kunna fitulun amma akai rashin sa'a ba kowa a kusa."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bankado jirgin sama da ake zargin ministan Buhari ya yasar a Jamus

"Daga ƙarshe dai, ya zama ba su da zaɓi sai su sauka a inda suke. Kuma matukin jrigin ya saukar da Jirgin lafiya ƙalau."

Dagaske mutum 6 sun jikkata?

Kakkain yan sanda ya ƙara da cewa babu wanda ya ji rauni daga cikin yan sanda dake cikin jirgin.

"Gaskiyar abin da ya faru shi ne lokacin da jirgin ya kusa kaiwa ƙasa, wutsuyarsa ta bugi wata bishiya. Wannan ne kaɗai matsalar da ta faru."
"Helikwaftan na ɗauke da mutum shida amma babu wanda ya ji rauni, kuma babu wata babbar matsala da jirgin ya samu."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

Wasu yan fashi da makami ɗauke da bindigu sun farmaki motar dakon kuɗi ta wani Banki da har yanzun ba'a gano ba.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun samu nasarar fasa motar, kuma sun yi awon gaba da adadi mai yawa na kuɗi a kan hanyar Otor-Owhe, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262