Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

  • Mallam Adamu, ministan ilimi ya yabawa kokarin gwamnatin Abdullahi Ganduje na jihar Kano kan yadda take tafiyar da lamarin kisan gillan da aka yiwa Hanifa
  • Ministan ya bayyana cewa suna bibiyar lamarin sosai domin ganin an yi adalci tare da kwato mata hakkinta
  • Ya bayyana abun da makashinta ya yi a matsayin cin mutuncin malamai gaba daya

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Minstan ilimi na kasa, Mallam Adamu Adamu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano kan matakan da ta dauka domin magance lamarin mutuwar Hanifa Abubakar, yar shekaru 5 da malaminta ya kashe ta.

Adamu wanda ya yi magana ta hannun daraktan labarai kuma jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Mista Ben Goong, a Abuja, ya yi Allah wadai da kisan Hanifa da malaminta, Abdulmalik Tanko ya yi bayan ya sace ta.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi
Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ministan ya kuma ce yana sanya idanu sosai kan ci gaban domin tabbatar da ganin cewa an hukunta wanda ake zargin, Pulse.ng ta rahoto.

Kafin mutuwarta, Hanifa, ta kasance dalibar makarantar Noble Kids Academy, wanda ke kwanar Dakata a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan ya ce:

“Muna zuba ido sosai a kan wannan Abun bakin ciki na kasa kuma muna da ra’ayin ganin an yi adalci.
“Idan yaro ba zai tsira ba a hannun malaminsa, a ina ne zai tsira.
“Wannan cin mutunci ne a kan dukka masu koyarwa kuma dole ne a hana sake faruwar haka.
“Muna mika ta’aziyya ga iyayen wannan yarinya da bata ji ba bata gani ba kuma muna addu’an Allah ya basu hakuri ta yadda ya dace.”

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Kara karanta wannan

Uwargida ta dannawa mijinta dutsen guga har lahira don ya dirkawa wata ciki

A baya mun ji cewa iyayen mutumin da ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekaru 5, Abdulmalik Tanko, sun gudu sun bar gidansu kan tsoron kai masu farmaki.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci yankunan Tudunwada da Tudun Murtala inda daga nan ne Abdulmalik ya fito kuma a nan ne gidansu yake, makwabta sun gaza bayar da bayani kan inda iyayensa suka shiga.

Majiyoyi na kusa da iyalan sun bayyana cewa an yi yunkurin kaiwa iyayen Abdulmalik hari sakamakon sacewa da kashe Hanifa da ya yi. Wannan lamari ya sa iyayensa suka gudu suka bar gidansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng