Da Dumi-Dumi: Babban Sarki da gwamna ya tsige daga kujerarsa ya rigamu gidan gaskiya

Da Dumi-Dumi: Babban Sarki da gwamna ya tsige daga kujerarsa ya rigamu gidan gaskiya

  • Basaraken Masarautar Akure, babban birnin jihar Ondo, Adesina Asepoju, wanda aka tunɓuke daga kan karagar mulki, ya kwanta dama
  • Masarautar ta fitar da sanarwan cewa tsohon Oba (Sarki) ya rasu ne a wani Asibitin kuɗi dake Abuja, da safiyar Alhamis
  • Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, shi ne ya sauke basaraken saboda wani rikici

Ondo - Sarkin masarautar Akure, babban birnin jihar Ondo, wanda aka sauke daga kujerarsa, Adesina Adepoju, ya riga mu gidan gaskiya.

Wannan an ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin iyalan masarautar Adesina, Prince Dapo Adepoju, ya fitar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa tuɓaɓɓen tsohon sarkin, Adepoju, ya rasa rayuwarsa ne ranar Alhamis, bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya a wani Asibitin kuɗi dake babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata ya sanar da kudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Jihar Ondo
Da Dumi-Dumi: Babban Sarki da gwamna ya tsige daga kujerarsa ya rigamu gidan gaskiya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Vanguard ta rahoto wani sashin sanarwan ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Oluwadare Adepoju ya riga mu gidan gaskiya yau da safe 27 ga watan Janairu, 2022, bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu a wani Asibitin kuɗi dake Abuja."
"Kafin rasuwarsa, tsohon Sarkin wanda ake kira 'Oba' ya yi addu'ar samun zaman lafiya a cikin masarautar Akure. Yace ya yi iya kokarinsa wajen kare martabar mutanen dake karkashinsa lokacin da yake kan sarauta."

Sanarwan ta ƙara da cewa marigayin kafin rasuwarsa ya roki al'ummar Masarautar Akure su haɗa kan su wuri ɗaya kuma su zauna lafiya.

Wane gwamna ne ya tsige shi?

Tsohon gwamnan jihar Ondo da ya gabata, Olusegun Mimiko, shi ne ya tsige Marigayi Adepoju, wanda ya jagoranci masarauta na tsawon shekara biyar.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bisa wani rikici da ya shiga tsakanin marigayin da matarsa, wanda ya yi sanadin mutuwar auren su.

Kara karanta wannan

Najeriya ce ta 1 cikin jerin kasashen Afrika da ake amfani da man Bilicin, Sabon Bincike

A wani labarin kuma Mutumin da ya kashe Hanifa yar shekara 5 a Kano, ya faɗi firar da suka yi ta karshe bayan ya shayar da ita guba kafin ta karisa mutuwa

Shugaban makaranta, Abdulmalik Tanko, wanda ya sace Hanifa kuma ya kashe ta, ya faɗi firar da suka yi kafin ta karisa mutuwa.

Malamin yace ya yi amfani da robar madara ta yara 'Bobo' wajen zuba wa Hanifa guba, kuma ya yaudareta ta sha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: