Gwamnan PDP ya bankado jirgin sama da ake zargin ministan Buhari ya yasar a Jamus
- An jefa manyan zargi a kan Rotimi Amaechi, ministan sufuri, a kan yin nauyin baki dangane da dukiyar jihar Ribas
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ne ya zargi Amaechi da barin jirgin saman jihar a kasar Jamus tun 2012
- Gwamnan jihar Ribas ya zargi ministan da kin sanar da shi batun jirgin a shekarar 2015 bayan ya gaje shi
Gwamnatin Nyesom Wike ta bankado wani jirgin saman jihar sa a kasar Jamus wanda gwamnatin Rotimi Amaechi ta bari a shekarar 2012.
A wani rahoto da ThisDay, Wike ya ce babban abin damuwa ne yadda Amaechi ya bar dukiyar jihar sa a can wajen Najeriya ba tare da ya rubuta wani rahoto ba kusan shekaru 12 kenan.
Wike ya yi wannan bayanin ne yayin da ya jagoranci wasu wakilai don wani taro da manajan bunkasa sana’o’i na General Atomics Aerotec a Munich, kasar Jamus, Markus Froetschi.
Ya yi bayani dangane da jirgin inda ya ce gwamnan da Amaechi ya gada, Peter Odili, ne ya siya jirgin kuma idan za a dawo da jirgin sai an kashe a kalla Euros miliyan 300.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
ThisDay ta ruwaito cewa, Wike ya yi mamakin yadda Amaechi bai taba sanar da shi labarin jirgin ba tun bayan mika masa mulkin da ya yi a 2015, kuma jirgin ya wuce watanni 6 na bincike.
Yayin yi wa Froetschi magana, gwamnan ya ce:
“Lokacin da na hau kujerar gwamna a 2015, ba mu da labarin cewa jirgin mu ne. Sai bayan bincike muka gano Legacy 600 na jihar mu ya na RUAG, General Atomics.
“Mun yi kokarin yin magana da ku wanda kuka amince. Don haka muna so mu yi muku godiya a kan yadda ba ku boye mana komai ba, saboda dukiyar gwamnatin jihar mu ce.
“Gwamna Peter Odili ne ya siya jirgin a shekarar 2003, a 2007 kuma ya mika wa gwamnan da ya gaje shi wanda yanzu haka ministan sufuri ne, Rotimi Amaechi. Lokacin yana gwamna a 2012 ya kawo jirgin nan kuma bamu san dalilin sa na yin hakan ba.”
Kuma mun san dai idan duba jirgin za a yi ba zai wuce watanni 6 ba, amma ya kamata ne a mayar da shi Najeriya a farkon shekarar 2013, cewar Wike.
Asali: Legit.ng