Jiragen yakin Najeriya sun kashe babban kwamandan ISWAP, Mallam Ari da sauransu

Jiragen yakin Najeriya sun kashe babban kwamandan ISWAP, Mallam Ari da sauransu

  • Jiragen yakin sojojin saman Najeriya sun ragargaji yan ta'addan ISWAP a jihar Borno
  • A yayin harin, an yi nasarar kashe babban kwamandan ISWAP mai kula da Kirta Wulgo, Mallam Ari da sojojin-haya da ke kera masu bama-bamai
  • Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai hare-haren ta sama

Borno - Jiragen yakin rundunar sojin sama karkashin Operation Hadin Kai sun farmaki wajen wani taro na kwamamdoji da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno inda suka kashe yan ta'adda da dama.

An tattaro cewa an kashe babban kwamandan ISWAP mai kula da Kirta Wulgo, Mallam Ari da sojojin-haya da ke kera wa yan ta'addan bama-bamai a yayin luguden wuta ta sama.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

Jiragen yakin Najeriya sun kashe babban kwamandan ISWAP, Mallam Ari da sauransu
Jiragen yakin Najeriya sun kashe babban kwamandan ISWAP, Mallam Ari da sauransu Hoto: PRNigeria
Source: UGC

Jaridar Thisday ta rahoto cewa an bayar da umurnin kai harin ta sama ne bayan bayanan sirri sun nuna cewa akwai yan ta'adda sama da 40 a yankin arewa maso gabashin Kirta Wulgo, kusa da inda ake zargin ISWAP sun kafa tuta.

Wata majiyar tsaro ta ce:

“An kuma gano wasu dauke da makamai a kusa da wani gini da ke kusa, wanda hakan ke nuni da cewa mai yiwuwa ginin ne ya samu babban harin ta’addanci.
“Bayan harin da aka kai ta sama, an ga wasu daga cikin ‘yan ta’addan da suka tsira suna kokarin kashe gobarar da ta tashi yayin da wasu kuma suka ci kafar kare."
“Hakika, gine-ginen da ke yankin sun kone sosai kuma sun lalace.
“An kashe mayakan ISWAP da dama a harin da aka kai ta sama ciki har da Malam Ari, wanda ake kira da Fiya na Kirta Wulgo."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da hatsabibin ɓarawo dauke da IPhones 16, kwamfuta da wasu kayayyaki a Oyo

Kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da kai hare-haren amma bai ce komai ba game da yawan mutanen da lamarin ya cika da su, rahoton BBC Hausa.

Sojoji sun yi kaca-kaca da mafakar ISWAP, sun ragargaji 'yan ta'adda

A gefe guda, mun ji cewa Sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan ISWAP a wani yankin jihar Borno, inda suka lalata mafakar 'yan ta'addan.

A wata sanarwar da rundunar ta soji ta yada a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa, aikin ya yiwu ne karkashin aikin share fage da sojoji ke yi a yankin.

A cewar sanarwar, dakarun rundunar 401 Special Forces Brigade da 19 Brigade Baga ne suka gudanar da aikin a ranar Talara 25 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng