A Najeriya: Yadda matashi dan shekaru 17 ya juya N1000, ya zama miloniya a wata 6
- Wani matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce bayan da ya bayyana kansa a matsayin miloniya yana da shekara 17
- Prosperity Olorunfemi ya tafi soshiyal midiya inda ya bayyana labarin nasarar da ya samu kuma ya ja hankalin mabiyansa da dama
- Matashin ya ce ya fara sana’arsa ne da N1,000 kacal, amma yanzu yana alfahari da Naira miliyan daya a tsawon watanni 6 na kasuwanci
Wani matashi dan Najeriya mai suna Prosperity Olorunfemi ya tafi shafin LinkedIn domin ya bada labarin yadda yake samun nasara a kasuwancinsa. Ya ayyana kansa a matsayin miloniya yana dan shekara 17.
Prosperity ya ce ya fara kasuwancinsa ne da kudi naira 1,000 kacal, lamarin da ya girgiza mutane da dama.
A cewarsa:
“Jiya na yanke shawarar bin diddigin bayanan kudi na. Kuma na gano cewa kasuwancina ya kawo zunzurutun kudi har Naira Miliyan 1.1 a jimlace a cikin watanni 6. A gaskiya ban taba tsammanin haka ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A koyaushe ina kiyasin kusan Naira 500,000. Amma ganin haka a daren jiya, na kusa shakewa saboda murna. Na dauki wasu matakai a watan Yuli lokacin da na fara da Naira 1,000 a asusun banki na. Na yi farin ciki da murnar wannan gagarumin ci gaba. Zan iya yin alfahari da kiran kaina a matsayin miliyoniya da ya kai kansa a 17."
A wata tattaunawa ta daban da Legit.ng Olorunfemi ya bayyana cewa ya samu matsala wajen samun waya a lokacin da ya ke son fara sana’arsa saboda iyayensa sun ki ba shi waya, saboda karancin shekarun sa.
A kalamansa:
"Lokacin da na kammala makarantar sakandare a 2019, na yi imani da yiwuwar samun kudin shiga ta yanar gizo. Amma abin da ya hana shi waya ne, ban samu waya ba duk kokarin da nayi amma iyayena ba su yarda da hakan ba a lokacin."
“Daga baya a 2021, mahaifiyata ta ba ni wayar da ta yi amfani da ita da kuma mai matsala, sai na fara yin kasuwanci a yanar gizo, a watan Yulin 2021, na aro kudi daga wajen wani abokina don in fara sana’a ta, na sayi earpod daga China na sayar da su ta yanar gizo ga mutane."
Martanin mabiyansa
Da yawa daga cikin mabiyansa sun bayyana ra'ayoyinsu game da labarin.
Duba kasa mun tattaro kadan daga ra'ayin mabiyansa:
Salem Andero ya ce:
"Kai, ina taya ka murna, Prosperity Olorunfemi O. Ina bukatar in bi wannan labarin a hankali. Ka ci gaba da yin abin da kake yi dan'uwa, ka zama abin koyi ga tsararrakin ka."
Mary Makinde ta ce:
"Wow, lallai wannan abin mamaki ne, ka burge sosai. Ina taya ka murna."
Elizabeth Aliyu ya ce:
"Wow, ina taya ka murna, ka zaburar dani in kara kaimi."
A wani labarin daban, a zamanin nan, wayoyin tafi da gidanka sun zo da abubuwa masu yawa ga mutane da yawa.
Wani dalibi dan kasar Indonesiya, Sultan Gustaf Al Ghozali, ya shiga wata duniyar fasahar mai sarkakiya, inda ya sayar da hotunansa na selfie a kan kudi naira miliyan 415. Hakan ya sa ya zama miloniya dare daya.
Dalibin mai shekaru 22 na Kimiyyar Kwamfuta ya canza kusan dukkanin hotunansa guda 1,000 zuwa fasahar kadarar crypto ta NFTs.
Asali: Legit.ng