Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa
- Babban jigon PDP kuma mamallakin tashar AIT yace Alhaji Atiku Abubakar kadai zai iya kada APC a 2023
- A cewarsa, Atiku shekaru hudu kadai zai yi ya sauka idan ya samu nasarar danewa karagar mulki
- Yace bayan shekaru hudun Atiku, za'a baiwa yan kudu maso gabas daman gabatar da dan yankinsu
Abia - Shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Cif Raymond Dokpesi, ya nemi yan Najeriya su zabi Atiku a 2023 saboda shekaru hudu kadai zai yi ya sauka.
Yace idan aka zabi Atiku kuma yayi shekaru hudu, yan yankin kudu maso gabas zasu samu daman gabatar da shugaban kasa a 2027.
Dokpesi ya bayyana hakan ranar Litinin a garin Umuahia, jihar Abia, rahoton Punch.
Yace Atiku ne mutumin da ya dace a marawa baya don kwace mulki daga hannun gwamnatin APC.
Yace rashin baiwa Arewa damar mulki a 2015 ya sa PDP ta fadi zabe a shekarar.
A cewarsa:
"Jam'iyyarmu ta yarda da tsarin kama-kama na ofishin shugaban kasa tsakanin Arewa da kudu na wa'adi biyu, shekaru takwas."
"Da muka shiga zabe kanmu a rabe, mun fadi. Shi yasa muka yi nazarin cewa don kwace mulki daga hannun APC, muna bukatar dan takara mai karfi daga Arewa."
"Tun da an ce Arewa maso gabas da kudu maso gabas ne yankuna biyu da basu taba yin shugabancin kasa ba. Mun yi tunanin Atiku, wanda dan Arewa maso gabas ne, shine dan takara mai karfi."
Gargadin wasu ga PDP: Kada ku ba 'yan shekara 70 tikitin takarar shugaban kasa a 2023
Wata kungiyar matsi da ke da alaka da jam’iyyar PDP ta yi gargadi kan bayar da tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ga duk wanda ya dara shekaru 70 da haihuwa.
Yayin da ta fitar da shawarar kayyade shekarun duk wanda zai karbi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Action 2023, ta ce samun dattijo a matsayin dan takarar jam’iyyar zai karya nasasar jam’iyyar ta samu nasara a zaben.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Rufus Omeire, Action 2023 ta ce ya kamata jam’iyyar PDP ta kara kaimi ta hanyar haskaka masu neman takarar da suke tsakanin shekaru 50.
Asali: Legit.ng