Kai ka kashe mahaifi na, Yaron Abiola ya yiwa AbdulSalami Abubakar martani

Kai ka kashe mahaifi na, Yaron Abiola ya yiwa AbdulSalami Abubakar martani

  • Daya daga cikin 'yayan marigayi Abiola ya yi raddi ga Janar AbdulSalami Abubakar kan jawabinsa
  • Jamiu Abiola ya ce ya kamata AbdulSalami Abubakar ya san ya tsufa yanzu kuma ya rika fadin gaskiya
  • Cif Abiola ne wanda ya lashe zaben shugaban kasan 1993 karkashin jam'iyyar SDP amma Babangida yayi watsi da zaben

Legas - Iyalan marigayi, Cif MKO Abiola, sun caccaki tsohon shugaban kasa, Janar AbdulSalami Abubakar bisa kalaman da yayi kan mutuwar mahaifinsu.

Janar AbdulSalami a hirar da yayi kwanakin nan da TrustTV ya bayyana cewa babu wanda ya kashe Abiola, rashin lafiya yayi kuma ba guba aka bashi ba.

Abiola, wanda gwamnatin Janar Sani Abacha ta tsare, ya rasu yayin da ya ke tsare, wata daya tak bayan mutuwar Abacha.

Kara karanta wannan

Shekaru 24 da faruwar lamari, Janar Abdussalam ya fadi yadda Abiola ya mutu a daure

Gwamnatin Abacha ce ta kama Abiola bayan ya bayyana kan sa a matsayin shugaban kasa duk da mulkin soja a lokacin ta ki bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben 12 ga watan Yunin 1993.

Yaron Abiola ya yiwa AbdulSalami Abubakar martani
Kai ka kashe mahaifi na, Yaron Abiola ya yiwa AbdulSalami Abubakar martani Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin yaran Abiola, ya ce karya Janar AbdulSalami yake, gwamnatinsa ta hana baiwa Abiola magana da kulan da yake bukata.

Yace:

"Wannan abun ya faru shekaru 24 da suka gabata. Janar AbdulSalami ya kara tsufa yanzu. Na yi tunanin idan mutum ya tsufa tsoron Allah yake karawa."
"Game da mutuwarsa kuma, mutum na iya daukan alhaki ta hanyoyi biyu. Idan ka kashe mutum da hannuka kamar yadda aka kashe mahaifiyata, wanda Sajen Rogers yayi madadin gwamnatin Soja."
"Ko kuma ka kashe mutum a kaikaice ta hanyar watsi da shi kamar yadda aka yiwa mahaifina lokacin Janar AbdulSalami."

Kara karanta wannan

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

"Mahaifina na da ciwon zuciya kuma shugaban kasan na sane da haka. Kowa ya sani. Ko wadanda suka hadu da shi jajibirin wafatinsa sun san cewa bai da lafiya kuma meyasa ba a kula da shi yadda ya kamata ba."

Abdulsalami: Rawar da Babagana Kingibe ya taka bayan mutuwar MKO Abiola

Janar Abdulsalami Abubakar, tsohon shugaban kasa, ya bayyana wasu abubuwa da suka faru bayan mutuwar Chief Moshood Kashimawo Olawole wanda aka fi sani da MKO Abiola.

Janar din mai ritaya ya sanar da rawar da Ambasada Babagana Kingibe ya taka wurin bayyana labarin mutuwar Abiola ga iyalansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng