Da duminsa: FG ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani
- Gwamnatin tarayya ta dakatar da kokarin cire tallafin man fetur har sai yadda hali ya yi bayan yunkurin haka da ta ke ta yi
- Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsari na kasa, ta sanar da hakan bayan ganawar da ta yi da Lawan, Kyari da Sylvia
- Da farko gwamnatin tarayya na yunkurin cire tallafi kan dukkan kayayyakin man fetur nan da watan Yulin shekarar nan
Majalisar dattawa, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani.
Kamar yadda TheCable ta ruwaito, gwamnatin ta shirya dakatar da biyan tallafi kan kayayyakin man fetur daga watan Yulin wannan shekarar.
Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsarin kasa, ta sanar da hakan a wani taro da aka yi a majalisar dattawan kasar nan a Abuja a ranar Litinin, TheCable ta ruwaito hakan.
Shugaban majalisar dattawan, Ahmed Lawan tare da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva gami da manajan daraktan NNPC, Mele Kyari, duk sun halarci taron.
A makon da ya gabata, Lawal ya ce Buhari bai bayar da umarnin cire tallafin man fetur ba, inda ya ce mazabun su suna bayyana damuwar su a kan sabuwar dokar.
Majalisar tattalin arziki ta kasa, NEC, ta ce ta na duba shawarar kwamitin rikon kwaryar ta, wanda ta bukaci a saisaita farashin man fetur zuwa N302 na lita daya.
TheCable ta ruwaito cewa, tallafin man fetur ya lamushe N1.43 tiriliyan a 2021, inda ya wabce kudin shiga zuwa asusun tarayya ya kai N542 biliyan, faduwa warwas kan N2.51 da aka saka san samu.
Ministan kudi ta ce gwamnati ta sake duba hukuncin ta bayan majalisa ta amince da kasafin shekarar 2022.
Ahmed ta ce tallafin man fetur da aka ware a kasafin shekarar 2022 zai rufa daga watan Janairun shekarar ne zuwa watan Yuni.
Ta kara da cewa, bayan zantawa da masu ruwa da tsaki saboda tsananin tashin farashin kayayyaki da kuma wuyar rayuwa, za a sake samar da yadda za a yi na tallafin man fetur din har a wuce watan Yunin.
Kamar yadda tace, a bayyane ya ke cewa idan aka cire tallafin man fetur a kasar nan, za a fada cikin mawuyacin halin tashin gwauron zabin farashin kayayyaki.
Asali: Legit.ng