Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta

Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta

  • Kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin cafke tsohuwar ministan Man Fefur, Diezani Alison Madueke, don gurfanar da ita
  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta na tuhumar Diezani da sama da faɗi da dukiyar ƙasa, amma ta yi biris, ta ɓoye a Burtaniya
  • Wannan umarnin zai baiwa yan sandan kasa da ƙasa, INTERPOL, damar kama tsohuwar ministan kuma a kawo ta Najeriya

Abuja - Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta bada umarnin kamo tsohuwar ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Alkalin kotun, mai Shari'a Bolaji Olajuwon, shi ya bada umarnin ranar Litinin, biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaƙi da cin hanci, (EFCC), Farouq Abdullah, ya gabatar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gwamna ya dakatad da Sarakunan gargajiya hudu kan sun yi laifi

Tsohuwar ministan man fetur, Diezani
Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A baya tsohuwar alƙalin kotun, Ijeoma Ojukwu, ta yi watsi da bukatar kamo Diezani, saboda gazawar EFCC wajen tabbatar da sammacin da aka aike wa tsohuwar ministan.

Ojukwu tace:

"A gani na sammacin da aka baiwa tsohuwar ministan zai baiwa ofishin AGF damar taso keyarta zuwa Najeriya."

Sai dai bayan canza wa Ojukwu wurin aiki zuwa kotun tarayya dake Kalabar, sai Shari'ar ta koma hannun Olajuwon.

Amma Abdallah, ya shaida wa kotun cewa ofishin Antoni Janar na ƙasa (AGF) na bukatar umarnin kotun domin hukumomin tsaro su samu damar kawo ta gaban alƙali ta fuskanci shari'a.

Yadda zaman kotun yau Litinin ya kasance

A zaman shari'ar na ranar Litinin, Abdallah ya bayyana wa kotu cewa duk wani yunkuri na dawo da Diezani Najeriya ya ci tura lokacin da lamarin ke hannun Ojukwu.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

Da yake gabatar da bukatar da baki, yace akwai bukatar umarnin kame na kotu domin baiwa yan sandan ƙasa da ƙasa (INTERPOL) damar kamo ta zuwa Najeriya, ta fusƙanci tuhumar da ake mata a gaban kotu.

Daga nan sai alkalin ya ba da umarnin kama ta kuma ya ɗage zaman har sai lokacin da aka kama Diezani kuma aka gabatar da ita gaban kotu.

Ina tsohuwar ministan ta ɓuya?

EFCC tace Diezani, wacce ke fuskantar sharia kan sama da faɗi da dukiyar ƙasa, ta buya ne a ƙasar Burtaniya, ta yi biris da ƙarar da aka kaita, kamar yadda The Nation ta rahoto.

A cewar hukumar EFCC, wannan umarnin ne zai baiwa INTERPOL dama su kamo ta, ofishin AGF ya cike sharuɗɗa a taso ƙeyarta zuwa Najeriya.

A wani labarin kuma Aisha Muhammadu Buhari, ta goyi bayan hukuncin kashe Malamin makaranta da ya sace Hanifa kuma ya kashe ta da guba a Kano

Kara karanta wannan

Damfarar N299.86m: Kotu na neman wani tsohon dan takarar gwamnan Zamfara

Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta nuna goyon bayanta kan irin hukuncin da ya dace a yanke wa makashin Hanifa.

Uwar gidan shugaban tace tana goyon bayan hukuncin da Shiekh Abdallah Gadon Ƙaya, ya yi kira a yanke wa mutumin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262