Minista Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma
- Malam Isa Pantami, ya bayyana cewa taɓa hakkin kananan yara babban laifi ne dake tsokano fushin Allah mai girma
- Ministan sadarwa yace ko a ranar Lahira, lallashin kananan yara ake su shiga Aljanna sabida darajarsu, amma suna cewa sai sun ga iyayen su
- Ya kuma yi Addu'a Allah ya kawo zaman lafiya, ya kuma baiwa duk wasu iyalai da irin haka ta faru da su hakurin cin jarabawa
Abuja - Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana darajar kananan yara yayin da yake martani kan kisan Hanifa Abubakar a Kano.
Ministan, wanda babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce mutane na cin albarkacin kananan yara wajen tausaya musu da Allah ke yi.
A karatunsa na littafin Birrun Walidayya (Biyayya ga iyaye darasi na 12), wanda ya gabatar ranar Lahadi, Pantami yace a ranar Lahira lallashin ƙananan yara ake su shiga Aljanna.
Pantami yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na samu ziyarar iyalan yarinyar na musu ta'aziyya, kuma na musu Nasiha kan su fawwala ma Allah komai domin shi baya kuskure. Na san zafin birne ƴa, amma a sace ɗiyarka a ƙashe ta, ba zaka san zafin ba sai ta faru da kai."
Darajar yara da kuma masifun taɓa haƙƙin su
Sheikh Pamtami ya ƙara da cewa a ranar Lahira, kananan yara togewa suke a bakin Aljanna, ana lallashin su amma suna cewa ba zasu shiga ba sai da iyayen su.
Shin wace daraja kake tunanin yara na da shi a wurin Allah da har ake lallashin su kan su shiga Aljanna? Ai darajar ta fi ƙarfin yadda kake tunani, a cewar Pantami.
"Mutanen da ake cewa ku yi hakuri ku shiga Aljanna, suna a'a ba mu ga iyayen mu ba, ba ku zaton taba haƙƙin waɗan nan yaran gayyato fushin Allah ne?"
"Taba haƙƙin kananan yara babban laifi ne dake tsokano fushin Allah, Duk wanda ya san hatsarin wannan lamarin dole ya tausaya mana."
"Domin taɓa yara ya isa Allah ya hana al'umma duk wani alheri da take nema. Kuma masifa idan ta zo, ta na shafan wanda ya tsokano ta da wanda ba ruwansa."
Ya kuma yi wa iyalan Hanifa Abubakar Addua, Allah ya basu hakurin cin wannan jarabawar, ya kuma saka musu da wani abu mafi Alkairi.
Shin Hanifa ce kaɗai yarinyar da haka ta taɓa faruwa da ita?
Pantami ya ce akwai mutane da dama da jarabawa makamanciyar wannan ke faruwa da su amma ba wanda ya sani, saboda yanzun sai kana da wata daraja sannan za'a san abin da ya faru da kai.
Sai dai, Malmain ya yi addu'a ga duk iyayen da makamancin haka ya faru da su, tare da musu fatan Alkairi. Domin a cewarsa ranar Lahira kananan yara na ceton iyayen su zuwa Aljanna.
A wani labarin na daban kuma Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta goyi bayan kashe waɗan da suka ci zalin Hanifa a bainar jama'a
Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ɗauki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.
Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta kan hukuncin kashe mutumin da ya kashe Hanifa a bainar jama'a domin hakan ya zama darasi ga yan baya.
Asali: Legit.ng