Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi

Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi

  • Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya jajanta kisan Hanifa
  • Shekarau ya sha alwashin daukan muhimmin mataki da kan sa a kan kisan gillar da Abdulmalik Tanko ya yi wa yarinyar mai shekaru 5
  • Shekarau ya sha alwashin cewa, ba zai bar wannan kisan rashin imanin ba ya tafi a haka, ya yi addu'ar natsuwa da hakuri ga iyayen ta

Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya sha alwashin daukar mataki da kan sa kan kisan gillar da aka yi wa Hanifa, yarinyar da aka yi garkuwa da ita kuma daga bisani aka kashe a Kano.

Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar da Hanifa ke zuwa, ya tabbatar da kashe yarinyar bayan ya yi garkuwa da ita a watan Disamba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi
Aiki ga mai yin ka: Sanata Shekarau ya magantu kan kisan Hanifa, ya sha muhimmin alwashi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata takardar da hadiminsa na fannin yada labarai, Sule Yau Sule ya fitar a shafin sa na Facebook, Shekarau ya jajanta wa iyayen yarinyar tare da shan alwashin sai ya bi mata khadin ta.

Sanata da ya yi gwamnan Kano har sau biyu, ya ce:

"Wannan kisan rashin imanin ba za mu bar shi ya tafi haka ba", inda ya sha alwashin bibiyar lamarin har sai ya ga karshen sa.

Shekarau ya yi fatan Allah ya bai wa iyayen Hanifa juriya da hakurin wannan rashin.

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

A wani labari na daban, Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi rikici a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano, yayin da Fatima Maina, mahaifiyar Haneefa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka ce malaminta ya kashe, ta hango mutumin da ya yi garkuwa da diyarta.

Kara karanta wannan

Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

A baya an ruwaito yadda aka kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kawana, Kano, dangane da lamarin.

Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da Haneefa, kuma masu garkuwar suka bukaci a biya ta Naira miliyan 6 a matsayin fansa.

Yayin da yake kokarin karbar wani bangare na kudin fansan, jami’an tsaro sun cafke Tanko da wasu da ake zargi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng