AFCON: Kai tsaye Buhari ya kira zakarun Super Eagles, ya kara musu karfin guiwa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira 'yan wasan Najeriya na kungiyar Super Eagles tare da yaba musu kan kokarin da suke yi
- Ya ce gwamnatin tarayya ta na bayan su kuma suna ta samun nasara, ya na fatan za su cigaba da samun nasara tare da zame wa ababen alfahari ga Najeriya
- Shugaban Buhari ya ce ya kira kocin kungiyar kai tsaye tare da yin bidiyo da kyaftin Ahmed Musa da kuma jakaden Najeriya a kasar Kamaru
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan wasan kwallon Najeriya na Super Eagles da su dage tare da yin nasara a wasan da za su buga da kasar Tunisia wanda ake yi an AFCON.
A wallafar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafin sa na Facebook, ya wallafa hotunan wayar da suka yi tare da bidiyo da 'yan wasan a ranar Lahadi da safe.
Buhari ya yi kira ga zakarun da su dage tare da cigaba da bayyana kwazon su a gasar tare da zama ababen alfaharin kasar nan.
Kamar yadda shugaban kasan ya bayyana, ya yi farin cikin yin magana da Koci Augustine, Eguaven, kyaftin din kungiyar, Ahmed Musa, shugaban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick da jakaden Najeriya a kasar Kamaru, Janar Abayomi Olonisakin mai ritaya.
A cewar shugaban kasan:
"Na sanar da su cewa, "Kun zame mana ababen alfahari. Ku na ta samun nasara. Ku cigaba da samun nasarar. Gwamnatin tarayya ta na goyon bayan ku kuma ina godiya gare ku. Ina rokon ku da ku cigaba da sanya kasar alfahari."
Kamaru: Ahmed Musa ya gwangwaje Masallacin Garoua da tallafin $1500
A wani labari na daban, Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya gwangwaje wani masallacin Juma'a da ke Garoua a kasar Kamaru da tallafin $1,500 bayan idar da sallar Juma'a, Punch Sports Extra ta ruwaito.
Masallacin wanda ya ke kusa da sansanin 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya a Garoua, shi ne inda 'yan wasan ke sallah a kowacce rana tun bayan isar su yankin arewacin kasar Kamaru a ranar 5 ga watan Janairu.
Punch ta ruwaito cewa, ana sa ran wannan tallafin zai taimaka wa malaman masallacin wurin kammala ginin, wanda har yanzu ake kan yi.
Asali: Legit.ng