Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari
- Shugabar hukumar NPA da aka dakatar Hadiza Bala-Usman ta hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari
- An gano hoton haduwar tasu da suka yi a jihar Kaduna, kuma wannan shine karo na farko da ake ganinsu tare a bainar jama'a tun bayan dakatar da ita watanni takwas da suka gabata
- Sun hadu ne a lokacin da shugaban kasar ya kai wa Sarkin Zazzau, Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli, ziyarar ban girma
Kaduna - Dakatacciyar Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala-Usman ta hadu da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, 21 ga watan Janairu.
Watanni takwas kenan bayan da Buhari ya amince da dakatar da Hadiza domin bayar da daman yin bincike mai zaman kansa kan wasu zarge-zarge da ake mata.
An zarge ta da laifin karya ka’idojin kudin gwamnati na NPA a karkashin kulawarta. Tun bayan faruwar haka, sai aka nada Mohammed Bello Koko domin ya jagoranci hukumar a madadinta.
Leadership ta rahoto cewa wata kila Hadiza ta gana da Shugaban kasar a bayan fage amma dai wannan shine karo na farko da ake ganin hotonsu tare a bainar jama’a tun bayan sanar da dakatarwar tata.
Koda dai kwamitin da ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kafa domin binciken zargin da ake mata, bai riga ya gabatar da rahotonsa ba kan lamarin, ana ganin ba lallai ne Hadiza ya koma kan kujerarta ba.
Amma a wani hoto da ya bayyana, an gano dakatacciyar shugabar ta NPA tana zantawa da Shugaban kasar a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa sarkin Zazzau, Mai martaba Ahmed Nuhu Bamalli, a Zariya, jihar Kaduna.
Buhari ya ziyarci sarkin ne daga wani bangare na ziyarar aiki na kwanaki biyu da ya kai jihar a ranar Juma’a, 21 ga watan Janairu.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe ma suna a hoton tsaye kusa da Hadiza Buhari.
Abin da ya sa ake zargina da satar kudin NPA - Hadiza Bala Usman ta fito, tayi magana
A gefe guda, mun ji cewa tsohuwar shugabar hukumar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman ta kalubalanci duk wanda yake da hujja ya nuna ta karkatar da dukiyar gwamnati.
Jaridar The Cable ta rahoto Hadiza Bala Usman ta bayyana wannan ne a wani jawabi na musamman da ta fitar a ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022.
Hadiza Bala Usman ta ce ya zama dole tayi wannan bayani domin ta wanke kan ta daga zargin cewa NPA ta ki maida kudi cikin asusun gwamnati a lokacinta.
Asali: Legit.ng