Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya

Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya

Farfesan Renewable Energy and Molecular Physics, a jami'ar jihar Kaduna, KASU, Muhammad Sani Abubakar, ya rasu ya na da shekaru 67.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kafin rasuwar sa a ranar Juma'a, Farfesa Abubakar malami ne sashin Physics a jami'ar jihar Kaduna.

Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya
Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya. Hoto dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin tabbatar da rasuwar sa, kanin mamacin, Injiniya Abdulrazak Abubakar ya ce mamacin ya yanke jiki ya fadi a KASU a ranar Juma'a kuma aka gaggauta mika shi asibitin makarantar inda aka tabbatar da rasuwar sa.

Ya ce marigayin Farfesa, wanda aka birne kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, ya kai 'ya'yan sa makaranta da safiyar Juma'a kafin ya dawo gida kuma ya shirya ya tafi makaranta.

“Labarai biyu aka ba mu a kan aukuwar lamarin, amma ba mu da tabbacin wanne ne. Wasu sun ce ya na tafiya a kafar bene sai ya fadi. Wasu kuwa sun ce ya na tafe ne kawai ya fadi. An gaggauta mika shi asibitin makaranta inda aka tabbatar da mutuwar sa," yace.

Kara karanta wannan

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

Daily Trust ta tattaro cewa, marigayin farfesan ya yi karatun firamare a makarantar Firamare ta Danja, kafin ya karasa Makarantar Sakandare ta gwamnati da ke Funtua.

Kanin farfesan ya ce daga nan ne ya karasa Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin ya karasa Jami'ar Ohio da ke Amurka inda ya yi digirin digirgir din sa.

“Bayan dawowar sa gida, ya fara koyarwa a jami'ar Bayero da ke Kano yayin daga baya ya samu aiki a matsayin daraktan kwalejin kimiyya da fasaha na foliteknik ta Kaduna. Daga bisani ya zama mataimakin shugaban foliteknik din," yace.

Ya ce mamacin ya yi aiki a matsayin daraktan NBTE kuma mukaddashin sakataren kafin ya yi murabus.

“Bayan yin murabus din sa, an nada shi daraktan cibiyar ilimin fasaha karkashin NBTE, inda daga nan ya wuce jami'ar jihar Kaduna inda ya zama Farfesa."

Kara karanta wannan

Salihu Lukman: Martanin Tinubu ga masu caccaka ta bayan na yi murabus daga mukami na

Mamacin ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya goma da jikoki.

Allah ya yi wa mahaifiyar attajiri Dahiru Mangal, rasuwa

A wani labari na daban, Allah ya yi wa Hajiya Murja Mangal, mahaifiyar shahrarren attajiri dan jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.

Hajiya Murja ta mutu ne a daren Alhamis tana mai shekaru tamanin da biyar (85) bayan gajeruwar jinya. Majiyar Vanguard ta ce za'a gudanar da jana'izah bayan Sallar Juma'a yau 21 ga watan Junairu, 2022.

Alhaji Dahiru Barau Mangal ne mammalakin kamfanin Afdin Group, kamfanin jirgin Max Air, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng