Shan Wiwi na iya haifar da matsala ga kwakwalwan dan Adam, Sabon Bincike
- Sabon bincike ya bayyana illan da shan tabar wiwi ke yiwa kwalkwalwar dan Adam musamman matasa
- Farfesa a jami'ar Wisconsin dake Amurka ya ce wannan babban hujja ne dake nuna ya kamata a haramta shan wiw
- Hukumar NDLEA ta kara kaimi wajen damke matasan Najeriya dake ta'amuni da wiw
Amurka - Wani sabon bincike ya nuna cewa shan wiwi na iya haifar da matsala a kwakwalwan dan Adam - musamman wajen tunani, yanke shawara da magance matsaloli.
A bisa binciken da aka wallafa ranar Laraba, babban abinda ke gusar da tunani dake cikin ganyen wiwi, tetrahydrocannabinol (THC), na da illa ga kwakwalwa, rahoton CNN.
A wannan bincike, an gwada mutane 43,000 kuma an gano cewa wannan abu ya fi tsanani cikin matasa saboda kwakwalwarsu bata gama girma ba.
Mawallafin binciken, Alexandre Dumais, yace Wiwi na iya rage ilimi kuma cikin manya rage kaimi wajen aiki da tukin mota.
Yace:
"Bincikenmu ya bamu daman duba sassan kwakwalwa da Wiwi ke yiwa illa, wanda ya hada da sashen mayar da hankali, tuna karatu, koyan sabon karatu."
Hakazalika Farfesa Megan Moreno na jami'ar Wisconsin ya ce ayi gaggawa amfani da sakamakon wannan binciken wajen hana matasa amfani da wiwi.
A cewarsa:
"Wannan bincike na gabatar da hujja mai karfi kan illan shan Wiwi, kuma ayi amfani da shi wajen hujjan hana matasa amfani da shi."
"Iyaye su sani cewa 'yayansu dake amfani da Wiwi na illata waje mafi muhimmanci a jikinsu, kwakwalwa."
Kada ku kuskura ku zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni, Uwargidar Masari
Dr. Hadiza Bello Masari, Uwargidar Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ta yi kira ga al'ummar jihar kada su kuskura su zabi yan shaye-shaye matsayin shugabanni.
Dr Hadiza ta bayyana hakan ne ranar Lahadi yayinda ta kaddamar da cibiyar horo da wayar da kan yan kwaya a garin Musawa, jihar Katsina, rahoton ThisDay.
Uwargidar Gwamnan tace yadda wasu yan siyasa ke yi a ofis da kuma irin laifukan da suke tafkawa na da alaka da kwaya.
Asali: Legit.ng