Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano

  • Hukumar yan sandan ta tabbatar da damke shugaban makarantar da ya sace Hanifa Abubakar kuma ya kasheta
  • An sace Hanifa, Yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya kwanakin 46 da suka gabata
  • Kawunta Zubair Siraj ya bayyana cewa guba suka sanya mata a abinci bayan karbar kudin fansa

Kano -Mammalakin makarantar Noble Kids School dake jihar Kano ya shiga komar yan sanda kan laifin garkuwa da kashe dalibar makarantarsa, Hanifa Abubakar yar shekara biyar.

Yan'uwanta sun bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda suka je gidan iyayenta jajanta musu lokacin da aka sace ta.

Kawunta, Suraj Sulaiman, yace:

"Hawaye ya rika zubawa lokacinda ya ziyarci gidansu gaisuwar jaje."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Duk da biyan kudin fansan N6m, masu garkuwa sun kashe yarinyar da suka sace a Kano

Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano
Yadda Shugaban makaranta ya sace dalibarsa kuma ya kasheta a jihar Kano Hoto: DailyNigerian
Asali: Facebook

Hukumar yan sanda a Kano ta tabbatar da damke Malamin, Abdulmalik Tanko, wanda yayi garkuwa da ita.

Kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a jawabinda ya saki ranar Alhamis.

Yace bayan dogon bincike da bibiya, jami'an DSS sun damke Abdulmalik Mohammed Tanko da Hashim Isyaku, yan unguwar Tudun Murtala Quarters, karamar hukumar Nassarawa.

Yayin bincike, AbdulMalik ya amsa cewa Hanifa dalibarsa ce a makaranta kuma ya saceta kuma ya kasheta bayan ta ganeshi.

Wani sashen jawabin yace:

"Ya saceta kuma ya kaishi gidansa inda ya bukaci yan'uwanta su biya milyan shida (N6,000,000.00). A ranar 18/12/2021, yayinda ya lura ta ganeshi, yace ya bata guba ta mutu kuma suke birneta tare da wani Hashim Isyaku cikin makarantar dake Kwanar 'Yan Gana."
"Sun kai gamayyar jami'an yan sanda da DSS wajen. An tono gawar kuma aka kai asibitin Mohammed Abdullahi Wase dake Kano inda Likita ya tabbatar da mutuwarta."

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai zata kaddamar da bincike kan makamai 178,000 da suka yi batan dabo

Ya ce za'a garzaya da su kotu bayan kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng