Majalisar wakilai zata kaddamar da bincike kan makamai 178,000 da suka yi batan dabo
- Sama da bindigogi, harsasai, da wasu makamin yaki sun bata cikin lissafi a hukumar yan sandan Najeriya
- Odito Janar na tarayya ya bayyana hakan a rahoton da ya gabatar kwanakin baya
- Yanzu majalisar wakilan tarayya ranar Alhamis tace zata gudanar da bincike kan wannan lamari
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta yanke shawarar kaddamar da bincike kan lamarin makamai 178,459 da suka yi batan dabo a ma'ajiyar hukumar yan sandan Najeriya a 2019.
Wannan ya biyo bayan bukatar da mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisa, Toby Okechekwu ya shigar ranar Alhamis a zauren majalisa, rahoton DailyTrust.
Zaku tuna cewa Odito-Janar na kasa ya bayyana cewa bincike ya nuna akalla makamai 178,459 sun yi batan dabo a 2019.
Yayin gabatar da jawabinsa, dan majalisan ya ce bincike ya nuna adadin bindigogin AK-47 kimanin dubu 90,000 sun bata kawo Disamban 2019.
Yace:
"Daga cikin wannan adadi, bindigogin AK-47 guda 88,078 sun bata a lissafi, dogayen bindigogi da kanana 3,907 sun bata kawo Junairun 2020."
"Bayanan dake cikin rahoton sun nuna cewa manya a hukumar yan sanda sun ki ajiye lissafin adadin makaman dake hannunsu; kuma hakan rashin biyayya ne ga tsarin hukuma."
Bayan jawabin, majalisar ta yi kira ga Sifeto Janar na yan sanda ya dau matakin gaggawa wajen damke wadanda suka sace makaman hukumar.
Majalisar ta baiwa kwamitin harkokin yan sandan aikin gudanar da bincike kuma ta dawo bayan makonni hudu da rahoto.
Asali: Legit.ng