Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

  • Dr Hakeem Baba-Ahmed, Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa, ya ce ba a bukatar shugaban kasa da za a zaba saboda kabilanci a Najeriya
  • Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a birnin tarayya, Abuja
  • Mai magana da yawun kungiyar ta dattawan arewa ya bayyana cewa kara farashin man fetur zai kara jefa 'yan Najeriya cikin kunci don farashin kayayyaki za su karu

FCT, Abuja - Dr Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ya ce Najeriya bata bukatar shugaban kasa na kabilanci, Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed
Hakeem Baba-Ahmed: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Da ya ke jawabi wurin taron tattaumawa da Daily Trust ta shirya a Abuja, Baba-Ahmed ya koka kan yadda lamura ke kara zafafa a siyasan Najeriya gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Karin Labari: Gwamnan Arewa ya yi mubayi'a ga Tinubu, yace shi ya fi cancanta ya gaji Buhari a 2023

A jawabin da ya yi game da wahalhalun da ake fama da shi a kasar, Baba-Ahmed ya ce:

"Daya daga cikin abubuwa mafi muni da za ka iya yi domin kara fusata mutane kan matsalin rayuwa shine, kara kudin man fetur, farashin kayayaki, hakan na jefa mutane cikin tsananin damuwa kuma kana son yin zabe nan da wasu watanni?"

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164