Babbar magana: Gwamna ya sanya hannu ya doka mai tsauri ta hana kiwo a fili
- Gwamnan jihar Benue ya sanya sabbin dokokin da ke alaka da makiyaya da masu dabbobi a fadin jihar
- Ya ce ya sanya hannu a dokar hana kiwo a fili ta 2017, wacce ke haramtawa makiyaya kiwo sakaka a cikin gari
- Gwamnan ya kuma bayyana tara ga kowane nau'in dabba, kama daga kan saniya har zuwa kan tsuntsaye
Benue - Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya rattaba hannu a kan dokar hana kiwo a fili na 2017.
Majalisar dokokin jihar ta zartar da kudurin dokar ne a ranar Talata, bayan duban sashi da sashi na nazarin rahoton zaunannen kwamitin kan noma da albarkatun kasa na majalisar yayin zaman majalisar.
Tun da farko Ortom ya nemi a sake bitar ne bisa dalilin cewa babbar dokar tana da wasu gyararraki da ke bukatar bita ta yadda za a dakile masu rashin mutunta dokar.
An ruwaito cewa, a yanzu dokar da aka yi wa kwaskwarimar ta nuna cewa duk wanda aka samu yana safarar dabbobi da kafa a cikin birane ko yankunan karkara ko kuma wani bangare na jihar zai biya Naira 500,000 a matsayin tara ga wanda ya yi laifi na farko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Idan kuma aka kama mutum ya aikata laifin sau a karo na biyu zai biya N1 miliyan tare da sharuddan gidan yari da suka dace da zabin tara.
Dokar da aka yi wa kwaskwarima ta kuma tanadi daurin shekaru 14 a gidan yari tare da zabin biyan tarar N5m ga duk wanda ya tura yaro mai karancin shekaru domin ya karya doka tare da cin tara a bangare saurana dabbobi kamar haka:
- N50,000 kan kowace saniya
- N10, 000 kan alade
- N5,000 kan kowane akuya
- N1,000 kowane nau'in tsuntsu ko kaji.
Gwamnan ya ce dokar baya ta N2000 kowace saniya an sauya ta zuwa N50,000 bisa la’akari da halin da ake ciki da kuma kudin da aka kashe wajen kawo su da kula da su a cibiyar kebewar ta jihar.
Ya kara da cewa, yayin da sauran sassan dokar za su ci gaba da zama kamar da, wani yanki da aka yi wa gyaran fuska ya kunshi tsawon kwanaki bakwai ga masu dabbobin da aka kwace su yi da’awar mallakar dabbobinsu ko kuma a yi gwanjonsu.
Da ma majalisar dokokn jihar a baya-bayan ta sanya hannu kan wannan kuduri, yanzu kuma za ta fara aiki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Miyetti Allah ta ce farashin saniya zai koma N2m idan aka hana kiwo a fili
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana cewa farashin saniya na iya kai wa sama da naira miliyan biyu a jihar Legas idan aka amince da rattaba hannu kan dokar hana kiwo a jihar.
Sakataren shiyyar Miyetti Allah a Kudu maso Yamma ne ya bayyana haka, yayin zaman sauraron ra'ayoyi na kwana daya da majalisar dokokin jihar ta shirya kan dokar hana kiwo a ranar Laraba 8 ga watan Satumba.
Jaridar Punch ta ce majalisar dokokin jihar Legas a ranar Litinin ta aika da kudirin dokar hana kiwo a fili ga kwamitin aikin gona bayan da ta tsallake karatu na biyu.
Asali: Legit.ng