Rudani: Anata cece-kuce a Twitter yayin da mahaukaci ya yiwa wani kyautar kudi
- Wani mai tabin hankali ya bi ta mashaya ya wuce amma sai ya yanke shawarar dawowa ya ba wani mutum kyautar kudi
- Kai tsaye ya tunkari mashayar da mutumin yake zaune ya je ya ba shi kyautar N200 sabuwa kal, lamarin da ya mutumin tsoro
- Sai dai mutumin da aka yi masa karimcin ya ce yana tsoron taba kudin duk da cewa mutane sun bashi kwarin gwiwar ya dauka
Menene ma'anar haka idan mahaukaci ya ba ka kyautar kudi? To, wani dan Najeriya yana gab da ganowa saboda ya karbi kyautar kudi N200 daga hannun wani mai tabin hankali.
@RadicalYouthMan, mutumin da ya sami wannan kyautar yana zaune a wata mashaya ne sai kwatsam ya ga mutumin mai tabin hankali ya tunkaro shi da kyauta.
Ya bayyana labarin mutumin da ya albarkace shi da kyautar kudi a shafin Twitter cewa:
“Wani abu ne ya faru yanzu, wani mahaukaci ne kawai ya ciro ya ba ni ₦200, ina wannan mashayar unguwar da ke unguwarmu, wannan mahaukacin kawai ya shigo ya ba ni ₦200, na tambaye shi dalilin da ya sa? Ya ce, “Kawai na yi maka kyauta ne."
Mutumin ya ce yana tsoron taba kudin yayin da ya bar su a ajiye a kan teburin da aka gani a hoton da ya yada. Ya rubuta cewa:
"Tsoro nake kada na taba."
Martanin 'yan Twitter
Amma a sharhin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @Donhollar ya karfafa masa gwiwar daukar kudin, yana mai cewa:
"Kana gab da zama hamshakin attajiri na gaba a Najeriya.. Ka yi amfani da tsabar kudinka ka siyo abinci da ruwa ga mutumin. Babu tsoro."
Wani tsokaci na @BennyUmoren ya kuma karfafawa mutumin gwiwa ya karbi kudin:
"Ka dauka, zai bude muku kofofin kudi, mahaukata sun ga fiye da abin da za ku iya tunani fa."
Da yake mayar da martani, mutumin da ya karbi kyautar kudin ya ce ya kuma bai wa mai tabin hankali kudi da dama a baya, wanda hakan ya sa wasu ke ganin cewa zai iya zama lokacin biyansa ne yanzu.
@RadicalYouthMan ya rubuta a cikin sashin sharhi na Twitter cewa:
"Eh... To in siyo masa abinci da ruwa? Yaso ya tambaye ni ko nine mai siyar da giya a mashayar, cewar yana son siya, nace a'a, sai ya tafi, amma shi mahaukacin sananne ne a kusa da unguwar, na ba shi kudi da yawa."
A wani labarin, ‘yan Najeriya sun yi wa wani dan talla fatan alheri bayan da bidiyonsa da yake nuna kirkinsa ga fursunonin da ke cikin motar gidan gyaran hali ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta.
A cikin wani faifan bidiyon da aka yada a shafin Instagram, dan Najeriyan da ke sana’ar tallan ruwan sha ya tunkari wata motar gidan gyaran hali da ke dauke da fursunoni.
Da kayansa na ruwan kwalba a kansa, dan tallan ya mika wa fursunoni makudan kudade ta taga. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake cinkoson ababen hawa a unguwar Ajah da ke Legas.
Asali: Legit.ng