An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

  • Sarkin Minna ya dakatar da dagacin kauyen Allawa da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja bayan ya yi wa wata budurwa auren dole
  • Ba a auren dole ya tsaya ba, Malam Bello Haruna ya ci zarafin mahaifin budurwar sannan ya umarci 'yan sa kai da su lakada mata mugun duka
  • An dakatar da dagacin tare da maye gurbin sa da galadima bayan an aike masa da sammaci zuwa fada amma ya ki zuwa

Minna, Niger - Masarautar Minna ta dakatar da dagacin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, Mallam Bello Haruna, kan auren dole da kuma rashin biyayya ga masarautar.

A wasikar da masarautar ta aike ta hannun mataimakin sakataren ta, Usman Umaru Guni, kuma Daily Trust ta gani, ta ce basaraken ya yi wa wata yarinya auren dole, ya tozarta mahaifin ta kuma ya umarci 'yan sa kai da su lakada mata mugun duka.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Sarki ya dakatar da dagaci kan auren dole da ya yi wa budurwa, ya umarci 'yan sa kai su nada mata duka
Sarki ya dakatar da dagaci kan auren dole da ya yi wa budurwa, ya umarci 'yan sa kai su nada mata duka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ana zargin dagacin da rashin biyayya ta yadda ya ki amsa kiran da aka yi masa zuwa fadar sarki domin yin bayani game da korafin sa da aka kai.

Sarki ya ce wannan halayyar da basaraken gargajiyar ya nuna ya bayyana rashin nagartar sa a fannin mulki wurin tabbatar da zaman lafiya da cigaban yanki kamar yadda aka nada shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, masarautar ta sanar da galadima Allawa, Ahmadu Magaji a matsayin mukaddashin dagacin garin.

'Yan bindiga: Matawalle ya dakatar da wani dagaci a jihar

A wani labari na daban, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amince da dakatar da wani babban dagacin Gummi, Alhaji Abubakar Bala Gummi, (Bunun Gummi).

A takardar da babban sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Aliyu Bello Maradun yasa hannu, an dakatar da dagacin ne a take sakamakon zarginsa da ake da taimakawa wajen tabarbarewar tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Abin da yasa Gwamnatin Tarayya ba za ta dena karɓo rancen kuɗi ba, Lawan

"An dakatar da Alhaji Abubakar Gummi a take, har zuwa lokacin da za a kammal binciken a kan zarginsa da hannu cikin rasa rayukan jama'ae kauyen Karaye," takaradar ta ce.

Duk da haka, Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya nada kwamiti don bincikar dalilin kisan rayukan jama'ar Karaye duk da kuwa an samu sasanci a tsakaninsa da 'yan bindigar a watannin da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: