'Yan bindiga: Matawalle ya dakatar da wani dagaci a jihar

'Yan bindiga: Matawalle ya dakatar da wani dagaci a jihar

Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya amince da dakatar da wani babban dagacin Gummi, Alhaji Abubakar Bala Gummi, (Bunun Gummi).

A takardar da babban sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Aliyu Bello Maradun yasa hannu, an dakatar da dagacin ne a take sakamakon zarginsa da ake da taimakawa wajen tabarbarewar tsaro a jihar.

"An dakatar da Alhaji Abubakar Gummi a take, har zuwa lokacin da za a kammal binciken a kan zarginsa da hannu cikin rasa rayukan jama'ae kauyen Karaye," takaradar ta ce.

Duk da haka, Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya nada kwamiti don bincikar dalilin kisan rayukan jama'ar Karaye duk da kuwa an samu sasanci a tsakaninsa da 'yan bindigar a watannin da suka gabata.

DUBA WANNAN: Yadda bindigar shaida ta harbe lauya a kotu

Gwamnan ya yi alkawarin sabawa duk wani mutum ko kungiya da take kokarin lalata yarjejeniyar tsaron da gwamnatinsa ta shimfida.

Idan zamu tuna, tun bayan bullo da salon yarjejeniyar, an koma rayuwa lafiya kalau kuma tsaro ya dawo jihar. Mutane na yawonsu yadda suke so ba tare da firgici ko tsoron sacesu ko kashesu ba.

Amma kwatsam! Ranar Lahadi da ta gabata sai labarin ya canza. Wasu Fulani sun afkawa kauyen Karaye inda suka halaka mutane. An gano cewa fansar kisan 'yan uwansu 9 ne da 'yan sa kai suka yi.

Kamar yadda rahoton hukumar 'yan sanda ya nuna, kungiyar 'yan sa kan sun kashe Fulani 9 da suke zarginsu da zama 'yan bindiga. Hakan ne ya jawo Fulanin suka afkawa kauyen har suka kashe mutane 14 tare da raunata mutane 10. Ba su tsaya a nan ba, sai da suka bankawa kauyen wuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel