Shari'ar Nnamdi Kanu: Mai gidan jaridar Sahara Reporters ya gamu da fushin 'yan sanda

Shari'ar Nnamdi Kanu: Mai gidan jaridar Sahara Reporters ya gamu da fushin 'yan sanda

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, kuma dan fafutuka Omoyele Sowore ya sha dakyar a harabar kotun Abuja
  • Wannan an zuwa ne yayin da ya halarci harabar kotun domin gane wa idonsa yadda za ta kaya a shar'ar Nnamdi Kanu
  • Ya zargi jami'an hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da kai masa hari, kamar dai yadda da yawan masu ra'ayi irin nasa ke yi

Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tarwatsa taron su Omoyele Sowore da wasu mutane da suka halarci babbar kotun tarayya don ganin yadda ta kaya a gurfanar da shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu, Punch ta ruwaito..

An ruwaito cewa Sowore wanda ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja a safiyar ranar Laraba an hana shi shiga harabar kotun kuma wasu ‘yan daba ne suka kai masa hari.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Kotu ta yi hukunci tsakanin Nnamdi da gwamnati, an ci gwamnati tara

Omoyele Sowore ya sha dakyar a hannun 'yan sanda
Shari'ar Nnamdi Kanu: Mai gidan jaridar Sahara Reporters ya gamu da fushin 'yan sanda | Hoto: saharareporters.com
Asali: Facebook

Bayan haka ne Jami'an Tsaro suka fara harba harsasai a iska wanda ya haifar da fargaba da rudani.

An ruwaito a baya cewa, Sowore, a ranar 21 ga watan Oktoba, 2021, ya ziyarci babbar kotun tarayya domin ganewa idonsa shari’ar da ake yi wa Kanu.

Sowore wanda aka kai wa hari a harabar kotun ya zargi jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da kai harin da aka kai masa.

An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati

Jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun tare hanyoyin da ke kaiwa harabar babbar kotun jihar Abia da ke kan titin Ikot Ekpene a Umuahia yayin da kotu za ta yanke hukunci a yau kan karar da shugaban IPOB, Mazi Nnamdi ya shigar kan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An tsaurara tsaro yayin da kotu za ta yanke hukunci tsakanin Kanu da gwamnati

Tun da karfe 7:00 na safe, an baza jami'an tsaro a kusa da harabar kotun, Vanguard ta rahoto.

Haka kuma an killace dukkan hanyoyin da ke kai wa ga kotun, wanda hakan ya tilastawa masu ababen hawa da masu tafiya a kafa bin wasu hanyoyin daban-daban.

An bukaci ‘yan jarida da ma’aikatan kotun da kuma mutanen da ke shiga harabar da su fito da katin shaida kafin a basu damar shiga harabar.

A wani labarin, wata babbar kotu a Umuahia ta umurci gwamnatin tarayya da sojojin Najeriya da su biya shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu N1bn bisa laifin mamaye gidansa a watan Satumban 2017, Vanguard ta rahoto.

Hakazalika, an umarci gwamnatin tarayya da Sojoji da su nemi gafarar Kanu bisa take masa hakkinsa na dan adamtaka.

Mai shari’a Benson Anya ya bayar da wannan umarni ne a yau a lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Kanu ya shigar a kan gwamnatin tarayya da sojoji da sauran su.

Kara karanta wannan

Za ayi sulhu tsakanin Tinubu da wanda ya kai shi kotu da zargin satar Naira Biliyan 20

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.