Kotun afil ta zabi ranar zama kan shari'ar dake tsakanin tsagin APC na Shekarau da Ganduje
1 - tsawon mintuna
Kotun daukaka kara dake Abuja ta zabi ranar Juma'a domin sauraron kara da aka shigar kan rikicin zaben shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kano.
A ranar Talata, Alkalan kotun sun dage karar zuwa ranar 21 ga Junairu, 2021 bisa bukatar lauyoyin da suke wakiltan bangarorin biyu, rahoton TheNation.
Lauyoyin sun hada da Nureni Jimoh (SAN), Mamman Lawan (SAN), da Steve Agbehi (SAN).
An daukaka karar ne bisa shari'ar da Alkali Hamza Muazu na babban kotun tarayya dake Abuja ya yanke ranar 30 ga Nuwamba, 2021, inda ya bayyana zaben tsagin Malam Ibrahim Shekarau matsayin sahihi.
Asali: Legit.ng
Tags: