Najeriya zata harba sabon tauraron dan Adam sararin samaniya, Farfesa Isa Pantami
- Bayan shekaru 11 da harba Sat1, Najeriya na shirin harba sabon tauraron dan Adam Sat2 a shekarar nan ta 2022
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ibrahim Ali Pantami ya bayyana hakan
- A cewarsa, an sanya kudin wannan sabon tauraro cikin kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari ya rattafa hannu
Abuja - Najeriya ta shirya tsaf don harba sabon tauraron dan Adam (Sat 2) cikin sararin samaniya don inganta karfin sadarwa a Najeriya, Minista Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron ziyara da tattauna da yayi da ma'aikatan hukumar tauraron dan Adam dake Abuja, rahoton Vanguard.
Farfesa Pantami ya ce ya samu dama daga wajen Shugaba Muhammadu Buhari na sayen sabon tauraron dan Adam.
Ya kara da cewa daga bisani, ya garzaya wajen Ministar Kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, don tabbatar da cewa an sanya kudin tauraron cikin kasafin kudin 2022.
Duk da cewa Ministan bai bayyana adadin taurarin da za'a saya da kudin ba, an tattaro cewa gwamnati ta ware N2.5 billion.
Da wanne Najeriya ke amfani yanzu?
Tauraron dan Adam da Najeriya ke amfani da shi yanzu Sat1 na gab da lalacewa.
Sat1R wanda aka harba samaniya tun 2011, zai lalace nan da shekaru hudu.
Zaku tuna cewa a 2017, gwamnatin tarayya ta bayyana shirin karban bashin $550m daga hannun bankin shiga da ficen China don gina sabbin taurarin dan Adam biyu.
A cewar NIGCOMSAT, Najeriya bata samu daman karban bashin ba saboda ta gaza biyan kashi 15% na kudin.
Asali: Legit.ng