ASUU zata maka gwamna El-Rufa'i a gaban kotu kan abinda yake shirin yi wa ABU

ASUU zata maka gwamna El-Rufa'i a gaban kotu kan abinda yake shirin yi wa ABU

  • Kungiyar ASUU reshen jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, (ABU) ta gargaɗi Elrufa'i ya dakatar da kudirinsa kan filayen jami'a
  • Shugaban ASUU-ABU, Farfesa Nasiru, yace kungiyarsu ba zata naɗe hannu tana kallo a yi wa jami'a ƙarfa-ƙarfa ba
  • Ya kuma baiwa masu siyan filayen gwamnati shawara kada su ɓannatar da kudinsu a banza wajen siyan filayen ABU

Kaduna - Ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU, reshen jami'ar Ahmadu Bello University (ABU Zariya), ta yi barazanar kai gwamnan Kaduna, Malam El-Rufa'i ƙara kotu.

Daily Trust ta ruwaito cewa ASUU na shirin ɗaukar wannan matakin ne matukar gwamnatin Kaduna ta cigaba da shirin kwace wa jami'ar filinta dake Mando, Kaduna.

Malam Nasiru
ASUU zata maka gwamna El-Rufa'i a gaban kotu kan abinda yake shirin yi wa ABU Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai a Zariya, shugaban ASUU-ABU, Farfesa Rabiu Nasiru, yace ƙungiyar ta samu labarin cewa gwamnati na shirin kwace fili mallakin kwalejin noma (Mando Campus, Kaduna), wacce ke karkashin ABU.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi awon gaba a da daliban jami'ar Tarayya a Nasarawa

Farfesan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hukumar KADGIS ta yi yunkurin gudanar da aikin duba filayen wurin da kuma yi wa filayen wurin iyaka, amma kwalejin ta ƙi yarda."
"Saboda haka, ASUU na gargaɗin gwamnan jihar Kaduna, ya dakatar da shirin take doka da kwace fili wanda mallakin jami'ar ABU ne."

ASUU ta gargaɗi masu sayan Filaye

Bayan haka, shugaban ASUU-ABU ya shawarci waɗan da gwamnatin ke shirin cefanarwa filin da kada su yi kuskuren sayan filaye a wurin domin za su tashi a tutar babu.

"Ga waɗan da suke shirin sayan filaye a wurin, muna ba su shawara kada su mika kuɗaɗen su kan filaye a wannan wurin, domin a banza kudin su zasu tafi."
"Ina mai ƙara jaddada cewa, kungiyar ASUU reshen jami'ar ABU ba zata runtsa ba har sai an warware wannan matsalar ta hanyar tabbatar wa ABU haƙƙinta."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta saka ranar babban gangamin taron ta na Arewa maso yammacin Najeriya

Kazalika Farfesa Nasiru, ya bayyana yadda ma'aikatar ayyuka da gidaje ta ƙasa ta yi kokarin amsar filin a hannun ABU amma ba ta samu nasara ba.

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Zamfara ya sanar da kudirin takarar shugaban ƙasaba 2023, ya samu gagarumin goyon baya

Wata kungiya ta sadaukar da kanta wajen yaɗa manufar takarar shugaban ƙasa na tsohon gwamnan Zamfara , Sani Yerima.

Kungiyar karkashin Yerima Support Organisation (YSO), ta raba wa mambobinta wayoyi da motoci domin fara yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262