Dakarun sojoji sun bindige mayakan Boko Haram sama da 40 a jihar Borno
- Sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan mayakan Boko Haram a garin Maina-Hari da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno
- Dakarun rundunar sun bindige mayakan kungiyar ta'addancin sama da guda 40 a ranar Asabar, 15 ga watan Janairu
- Mayakan sun yi yunkurin kaddamar da hari ne a yankin inda suka je da motocin harbi shida
Borno - Rahotanni sun kawo cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun bindige mayakan Boko Haram a garin Maina-Hari da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta rahoto daga wata majiya cewa dakarun rundunar Operations Hadin Kai ne suka bindige mayakan a lokacin da suka yi yunkurin kai hari babban garin da ke yankin kudancin Borno a ranar Asabar.
Da yake magana game da lamarin, Haruna Aliyu, wani mamba a kungiyar sa-kai ta CJTF, ya ce mayakan sun zo da motocin harbi guda shida, rahoton Aminiya.
Ya ce yan kadan daga cikin su ne suka tsere yayin da sojoji da yan sa-kai suka bude masu wuta.
"Mun sha karfin kungiyar yan ta'dannan a cikin mintuna 45. Wannan ne aiki mafi kyau da muka yi a baya-bayan nan, mun kashe ’yan Boko Haram sama da 40 a yau."
Har yanzu Yan Boko Haram ne suke da iko kan wasu kananan Hukumomi a Borno, Gwamna Zulum
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa har yanzu kananan hukumomi biyu na Abadam da Guzamala da ke jihar na karkashin ikon Boko Haram.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da kwamitin majalisar dattawa kan rundunar soji, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati, Maiduguri a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, Daily Trust ta rahoto.
Zulum ya nuna damuwa kan yadda yan ta'addan kungiyar ta ISWAP ke ci gaba da karuwa a yankin Kudancin Borno, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng