Yanzu-Yanzu: Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu
- Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun kai hari garin Mainahari kusa da Wakabiu a karamar hukumar Biu a Borno
- Wata majiya a garin ta tabbatar da cewa sun jefa bam misalin karfe 3 na rana sannan suka yi yunkurin shigowa garin don
- Sai dai zaratan dakarun sojojin Najeriya sun katse musu hanzari inda suka yi arangama suka kuma ci galaba a kansu suka kashe da dama cikinsu tare da kwace makamai
Borno - Mayakan kungiyar ta'addanci ta Islamic State West Africa Province, ISWAP, a ranar Asabar, sun kai hari Mainahari a kusa da Wakabu a karamar hukumar Biu ta Jihar Borno, The Punch ta ruwaito.
A cewar wata majiya daga barikin sojoji a Biu, 'yan ta'addan sun harba bama-bamai a kauyen misalin karfe 3 na rana.
Sai dai, dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan.
"Muna barikin sai muka fara jin karar bama-bamaii misalin karfe 3 da rana a yau. Sai muka ji wai suna kokarin shiga kauyen Mainahari ne da ke kusa da Wakabiu amma sojoji suna ankare kuma nan da nan suka far musu.
"Babu wanda ya mutu cikin sojojin amma mun ji cewa sojojin sun kashe yan ta'addan da dama, sun kwace mota mai dauke da bindiga da makamai da dama daga yan ta'addan da ke tserewa," wani farar hula a barikin ya shaidawa The Punch.
Wannan harin na zuwa ne bayan harin da ake ce yan ta'addan ISWAP sun kai garin Biu bayan kai hari cibiyar zaman lafiya da kwallejin yaki a Buratai kimanin kwana biyar da suka gabata.
Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.
Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.
Asali: Legit.ng