Idan har Tinubu ya zama Shugaban kasa zan bar Najeriya, Bode George ya lashi takobi

Idan har Tinubu ya zama Shugaban kasa zan bar Najeriya, Bode George ya lashi takobi

  • Tsohon Gwamnan jihar Ondo ya yi kira ga yan Najeriya suyi hattara da Tinubu ko kuwa suyi nadama
  • A cewarsa, Tinubu ba irin mutumin da za'a iya mikawa kasa irin Najeriya bane saboda kasheta zai yi
  • Bode George idan har Bola Tinubu ya zama shugaban kasa lokacin barinsa Najeriya ya yi

Tsohon Gwamnan jihar Ondo lokacin mulkin Soja, Cif Bode George, ya lashi takobin cewa idan har jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya zama Shugaban kasa zai kwashe kayansa ya bar Najeriya.

Bode George wanda babban jigon jam'iyyar PDP ne ya bayyana hakan a hirarsa da jaridar Vanguard.

A jawabinsa, yace Tinubu ba irin mutumin da za'a mikawa mulkin Najeriya bane saboda kashe kasar zai yi.

A cewarsa, babu alkhairin da Tinubu zai kawowa Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya su rika yi mana adalci kan lamarin tsaro, muna kokari:Shugaba Buhari

Yace:

"Zan bar Najeriya, saboda shi zai zama wakilinmu a idon duniya. Wani alkhairi zai kawo nan? Ba wai ina fadin wannan don na tsaneshi bane."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan ba irin mutumin da zamu mikawa babbar kasa irin wannan bane. Abin dariya zai zama a idon duniya. Ya kamata mu mayar da hankali kan wanda zai jagorancemu."
"Wadanda ke goyon bayansa sune wadanda suke amfana da kudinsa."

Bode George ya lashi takobi
Idan har Tinubu ya zama Shugaban kasa zan bar Najeriya, Bode George ya lashi takobi
Asali: UGC

Burin Tinubu ya gamu da cikas na farko, Shugaban Yarbawan Afenifere ya ki mara masa baya

Shugaban kungiyar Yarbawa na kasa watau Afenifere, Ayo Adebanjo ya yi martani a game da shirin Asiwaju Bola Tinubu na takarar shugaban kasa.

Cif Ayo Adebanjo ya bayyana cewa kungiyar Afenifere ba za ta marawa wani ‘dan takara daya baya ba, har sai an canza tsarin mulkin kasar kafin 2023.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

Adebanjo ya ce ba su yarda da tsarin mulkin da ake amfani da shi ba, don haka suke bukatar ayi gyara. Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng