Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa

  • 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun sake kai wani hari a kauyen Kautikari da ke kusa da garin Chibok a Jihar Borno
  • Maharan shigo garin cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da fuskantar wata turjiyya ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa mazauna garin da dama suna ta ficewa suna hijira zuwa garin Chibok domin su tsira da ransu da dukiyarsu

Borno - A kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.

Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da garin Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu

Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa
Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane 3, sun ƙona gidaje ciki har da makaranta da coci. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.

Ya ce sun shafe kimanin awa biyu a kauyen suna bi gida-gida a kauyen.

Majiyar ta ce:

"Sun taho da motocci biyar domin kai hari a kauyen Kautikari kuma suka fara harbi ta ko ina, mutane uku sun rasa rayyukansu sannan sun kona gidaje da yawa ciki har da coci da makaranta."

Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa mazauna kauyen sun tsere Chibok don su tsira da ransu.

Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu

Kara karanta wannan

Sarki a Arewa ya sha da ƙyar hannun matasa da suka kai hari fadarsa don ya gaza kare su daga harin ƴan bindiga

A wani labarin, mayakan kungiyar ta'addanci ta Islamic State West Africa Province, ISWAP, a ranar Asabar, sun kai hari Mainahari a kusa da Wakabu a karamar hukumar Biu ta Jihar Borno, The Punch ta ruwaito.

A cewar wata majiya daga barikin sojoji a Biu, 'yan ta'addan sun harba bama-bamai a kauyen misalin karfe 3 na rana.

Sai dai, dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164