Hukumar EFCC ta damke Lauyan bogi da yaje ofishinta karban belin wani madamfari
- Wani lauyan karya mai karfin hali ya garzaya ofishin hukumar EFCC don karban belin dan damfara
- Ashe da walhakin shima zai shiga hannu yayinda jami'an hukumar suka gane takardun bogi ya rike
- Hukumar tace za ta gurfanar da shi gaban kuliya
Legas - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke lauyan bogi, Adekola Adekeye, kan laifin kirkiran takardun bogi don damfara.
Kakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Abuja, rahoton NAN.
Ya ce asirin lauyan ya tonu ne lokacin da yaje ofishin hukumar karban belin wani dan damfara.
A cewarsa:
"A ranar 11 ga Junairu, 2022, ya zo ofishinmu na Legas karban belin wani mutumi da ake yiwa zargin damfara."
"Amma asirin Adekeye ya tonu lokacin da jami'ai suka bincike takardun da ya gabatar don karban belin mutumin."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sun je har gidansa don bincike
Uwujaren yace jami'an EFCC sun garzaya gidansa don gudanar da bincike kawai sai suka tarar takardun bogi na jami'ar jihar Legas.
"Yayinda aka gudanar da bincike gidansa, an gano takardun bogi na tun shekarar 2005," yace.
"Ya yi ikirarin cewa shine mai ofishin “A.A. Emmanuel & Co. Chambers”, da yake amfani wajen damfara kafin a damkeshi, Za'a gurfanar da shi a kotu."
Hukumar EFCC ta damke Janar din Soja na Bogi
EFCC ta damke wani Janar din Soja na karya kan zargin damfarar N270m (Milyan dari biyu da saba'in).
EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki tare da hotunan Sojan a shafinta na Tuwita.
Sojan Bogin mai suna Bolarinwa Oluwasegun ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya so ya zama Shugaban hafsan Sojin Najeriya.
Jawabin:
"Jami'ar hukumar EFCC na shiyar Legas sun damke, Bolarinawa Oluwasegun, wani Janar din Sojan karya wanda yayi ikirarin Buhari ya zabeshi matsayin Shugaban hafsan Soji da zargin damfarar N270m."
Asali: Legit.ng