Yan adaidaita sahu a Kaduna sun nemi afuwar Gwamnan Nasir El-Rufa'i

Yan adaidaita sahu a Kaduna sun nemi afuwar Gwamnan Nasir El-Rufa'i

  • Jami'an Gwamnatin jihar Kaduna suna bi suna kwace baburan adaidata sahu da suka saba dokar hana tuki da dare
  • Sakamakon haka sun kwace baburan Keke Napep da dama
  • Kungiyar matuka Keke Napep suna rokon Gwamnan yaji tausayi yayi musu afuwa ya basu baburan su

Kaduna - Shugabannin kungiyar matuka Keke Napep wacce akafi sani da kekunan adaidaita sahu a jihar Kaduna sun nemi afuwar Gwamnan jihar Kaduna bisa laifin da wasu mambobinsu suka yi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa ranar 2 ga Oktoba, Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa sabuwar dokar takaita hada-hadar Keke Napep daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma.

Jawabin neman afuwar direbobin na kunshe cikin takardar da Shugaban kungiyar, Aminu Ibrahim, ya saki a Kaduna.

Kara karanta wannan

Saboda tsabar gudu, Direban tirela ya kashe yara biyu a gaban shagon mahaifiyarsu

Yan adaidaita sahu a Kaduna sun nemi afuwar Gwamnan Nasir El-Rufa'i
Yan adaidaita sahu a Kaduna sun nemi afuwar Gwamnan Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ibrahim ya kuma roki gwamnatin jihar ta saki kekunan adaidaita sahun da jami'an gwamnati suka garkame.

Yace:

"Muna bada wannan hakuri ne sakamakon saba dokar da wasu mambobin kungiyarmu sukayi na tuka abubuwan hawansu don neman abinci."
"Bincikenmu ya nuna cewa yawancin wadanda suka saba dokar karfe 6 zuwa 7 na yamma ba da gayya sukayi ba."
"Cinkoson kan titi ne ke tilastawa direbobi da suke hanyar komawa gida daukar mata da marasa karfi masu shekaru."

Ibrahim ya ce kungiyar na aikin wayar da kan mambobinta bisa muhimmancin bin doka.

"Muna tabbatarwa Gwamnatin jihar cewa mambobinmu zasu bi dokar lokacin da aka tsayar", yace.

"Zamu cigaba da bada namu gudunmuwar wajen tabbatar da bin dokar Gwamnati."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng