Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

  • Shehu Sani ya bayyana ra’ayinsa dangane da tallafin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya bayar a jihar Zamfara
  • A nasa martanni, tsohon sanatan mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sani ya ce zai tuntubi abokinsa Dele Momodu domin ya kai tallafi ga wadanda hare-haren Neja da Kaduna suka shafa
  • A halin da ake ciki, Tinubu ya ziyarci jihar Zamfara domin jajanta wa Gwamna Bello Matawalle kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar

Jihar Kaduna - Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani kan tallafin Naira miliyan 50 da Bola Ahmed Tinubu ya bayar ga wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a jihar Zamfara.

Tsohon sanatan a martaninsa ta shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 14 ga watan Janairu, ya bayyana cewa zai tuntubi abokinsa, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Dele Momodu domin ya yi irin haka ga mutanen Neja da Kaduna.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: 'Yan bindiga sun zama jiha mai zaman kanta a cikin jihohin Arewa maso Yamma

Tsohon Sanatan Kaduna ya magantu kan kirkin Tinubu ga 'yan Zamfara
Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara | Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Ya rubuta cewa:

"Jagaban ya bayar da gudunmuwar N50m ga wadanda harin 'yan bindiga na Zamfara ya rutsa da su; Ina kokarin kiran abokina Momodu na sanar da shi wadanda harin Neja da Kaduna ya shafa."

A halin da ake ciki, mazauna kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara sun ce sun gano gawarwaki sama da 50 bayan harin da aka kai a farkon makon nan a wasu kauyukan jihar, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mazauna yankin sun ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wasu gawarwaki da wadanda suka jikkata.

Kungiyar Zamfara Circle ta taimakawa yan gudun hijra da kayan abinci

A wani labarin, kungiyar Zamfara Circle Initiative ta raba kayan abinci ga wasu jama'a jihar Zamfara da hare-haren yan bindiga ya tilasta musu guduwa daga muhallansu.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Wata 2 da suka gabata, Fashola yace Tinubu zai bayyana burinsa a watan Janairu

Wannan kungiyar da Barista Audu Bulama Bukarti ya jagoranci tara kudi ta fara rabon kayan abinci ga iyaye mata a jihar Zamfara.

A farko shekarar nan, Audu Bukarti, wanda dalibin Doktora ne a jami'ar SOAS dake Birtaniya ya koka kan irin halin da wasu mutane da yan bindiga suka fitittika daga muhallansu suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.