Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 daga hannun masu fasakwabri zuwa kasar waje

Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 daga hannun masu fasakwabri zuwa kasar waje

  • Jami'an hukumar kwastam na Seme sun yi nasarar kama haramtaciyyar man fetur lita 30,150 daga hannun masu fasakwabri
  • Jami'an hukumar masu sintiri ne suka yi karo da 'yan fasakwabrin a daren ranar Laraba suka gano man fetur din an boye cikin buhuna
  • Kwantrollan yankin Seme, Bello Mohammed Jibo, ya tabbatar da kamen yana mai cewa motar sintiri ta 'Buffalo' da aka siya musu ta taimaka musu shiga lunguna da sako

Seme Border - Jami'an hukumar Kwastam, na yankin Seme, a wani samamen cikin dare sun kama litar man fetur 30,150 da ake karkatar zuwa Jamhuriyar Benin, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne kusan makonni biyu bayan hukumar ta yi wani kame mai kala da wannan.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun kai hari Plateau Poly, sun kwashe dalibai

Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 da masu fasakwabri za su kai kasar waje
Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 da daga hannun 'yan smogal. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kwantrolla na yankin ya tabbatar da kamen

Kwantrollan yankin Seme, Bello Mohammed Jibo, ya ce an yi kamen na baya-bayan nan ne a ranar 12 ga watan Janairun 2022.

Daily Trust ta rahoto Jibo ya ce kamen na cikin kokarin da hukumar ke cigaba da yi ne na dakile masu safarar man fetur ba bisa ka'ida ba a yankin.

Ya ce jami'an hukumar a yankin, yayin sintiri da suka saba fita a yankin Seme da Badagry sun kama man fetur da yawa a cikin buhunna.

Ya ce an kwace kayayyakin an kai harabar ofishin rundunar, inda aka bincika sosai.

Ya ce:

"Binciken da aka yi ya nuna jarkokin man fetur 1005, kowannen su lita 30, daidai da lita 30,150; da ya kamata a biya musu haraji na N6,974,750.00."

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ginin wurin Ibada ya hallaka mutane suna tsaka da bautar Allah

Ya kara da cewa sabon mota kirar Landcruiser (Buffalo) da hukumar ta samar ya taimaka wa jami'an wurin aikinsu, domin kafin samun motar, jami'an ba su iya shiga lunguna amma yanzu suna iya shiga ko ina.

Tirelar Da Jami’an Kwastam Su Ka Biyo Ta Afka Wa Wata Mata Da Yaranta 3

A wani labarin, jami’an hukumar kwastam, NCS, a jihar sun biyo wata tirela wacce ta fada wa wata mata da yaranta uku a ranar Talata da dare cikin Ilorin, Daily Trust ta ruwaito.

Mummunan lamarin ya auku ne bayan wata daya da jami’an kwastam din su ka ci karo da wasu matasa a Ilorin yayin da su ke kokarin kama wata tirela wacce take cike da kayan fasa kwauri.

An samu bayanai akan yadda lamarin ya auku a daidai randabawul din garejin Offa kuma hakan ya yi sanadin cunkoso akan titin wanda aka kwashe sa’o’i ana yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164