Wata sabuwa: NDLEA ta titsiye biloniya Obi Cubana kan zargin safarar miyagun kwayoyi

Wata sabuwa: NDLEA ta titsiye biloniya Obi Cubana kan zargin safarar miyagun kwayoyi

  • Alamu sun nuna cewa, hankalin hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi ta koma kan biloniya kuma dan ashoshala, Obi Cubana
  • Bayan artabun biloniyan da hukumar yaki da rashawa a 2021, alamu na nuna cewa bai fara shekarar 2022 da sauki ba, tunda NDLEA sun hange shi
  • Hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyin ta ce ta gano Obi Cubana ya na da alaka da wasu manyan masu safarar miyagun kwayoyi a Malaysia da Indiya

Hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) a ranar Alhamis, 13 Janairu ta yi nasarar caafke shugaban kamfanonin Cubana, Obi Iyieghu, wanda aka fi sani da Obi Cubana.

Ana zargin sa da hada kai da hatsabiban masu safarar miyagun kwayoyi. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Obi Cubanan ya kai tsawon awa 5 a hedkwatar NDLEA da ke Abuja kafin a bada belinsa da umartar dawo dashi bayan wani lokaci.

Kara karanta wannan

Hular Tinubu ta yi daraja a kasuwar intanet, 'yan Najeriya sun yi tururuwa domin saye

Wata sabuwa: NDLEA ta tsitsiye biloniya Obi Cubana kan zargin safarar miyagun kwayoyi
Wata sabuwa: NDLEA ta tsitsiye biloniya Obi Cubana kan zargin safarar miyagun kwayoyi. Hot daga Hustle & Bustle
Asali: Facebook

Majiyoyi daga Facebook sun bayyana cewa wasu kudi da ke da alamar tambaya sun shiga asusun bankin Cubana daga wadanda aka kama dumu-dumu da laifin safarar miyagun kwayoyi daga Malaysia, Najeriya da India.

Ma'aikatan NDLEA da EFCC a halin yanzu suna cigaba da binciken Cubana da sana'arsa wanda ke nuna cewa akwai yuwuwar yana da sa hannu a safarar miyagun kwayoyi.

An bai wa fitaccen biloniyan damar komawa gida amma ya nemo shaidar da zai gabartar wa NDLEA.

An ga Cubana a bikin zagayowar haihuwar Ahmad Lawan

A ganin karshe, an ga Cubana a bikin zagayowar haihuwar Ahmad Lawan a Abuja inda aka ga Cubana a bayyane ya na taya Dr. Ahmad lawal murna a Abuja.

Bulaliyar majalisar dattawan Najeriya, Senator Orji Uzor Kalu ne ya tarbi baki a gidansa na Abuja, wanda shi ma ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani gida, uwa da jaririnta sun kone a Kano

Hakazalika, an ga hoton Obi Cubana tare da Kalun wanda a da can shi ne tsohon gwamnan jihar Abia.

EFCC ta saki Obi Cubana, attajiri mai facaka da dukiya

A wani labari na daban, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta sako attajirin mai facaka da dukiya, Obinna Iyiegbu, da aka fi sani da Obi Cubana.

Instigator PH, abokin aikinsa ne ya wallafa labarin sakinsa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Instagram a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng