Da Dumi-Dumi: Sojojin sama sun kwato yan kasuwan da yan bindiga suka sace a Kaduna
- Dakarun rundunar sojin sama (NAF) sun samu nasarar kwato mutum 26 daga cikin matafiyan da aka sace a hanyar Birnin Gwari
- Sojoji na musamman SF ne suka ceto mutanen yayin da suka bi sahun maharan zuwa cikin jeji a yankin Anguwan Yako
- Wannan na zuwa ne bayan wasu tsagerun yan bindiga sun sace yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna
Kaduna - Rundunar sojin saman ƙasar nan (NAF), tace dakarunta na musamman sun kwato mutum 26 daga cikin yan kasuwan da mahara suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da NAF ta fitar a shafinta na Facebook, ɗauke da sa hannun kakakinta, Air Commodore Edward Gabkwet.
Kakakin rundunar sojin yace dakarun na cikin aikin sintiri, sai suka gamu da motoci biyar babu kowa a ciki a Anguwar Yako.
Yace yayin da yan bindigan suka hangi sojojin sai suka tsere cikin daji tare da wasu daga cikin mutanen da suka sato, suka bar wasu anan.
Kakakin sojin yace:
"Dakarun na musamman (SF) na rundunar sojin sama (NAF) a yau 12 ga watan Janairu, 2022, sun kubutar da mutum 26 yayin da suke sintiri a kan hanyar Birnin Gwari-Kaduna."
"An ceto mutanen ne yayin da SF suka zo wuce wa ta wajen wasu motoci 5 da aka yasar a kan hanya, kofofin su a bude a Anguwar Yako, kuma ga dukkan alamu sace mutanen ciki aka yi."
"Ganin haka yasa dakarun SF suka fara dube-duba suka bi maharan har tsawon kilomita 3. Saboda ganin sojojin nan take mutum 3 daga cikin matafiyan suka fito daga cikin jeji."
Kakakin NAF ya ƙara da cewa yayin da jami'an SF suka ƙara matsa bincike a jejin sun gano mutane tawaga-tawaga har hudu, wadan da aka sato. Bayan dogon bincike a yankin, Sojojin suka gano mutum 26 jumulla.
Yadda yan bindiga suka sace su
Yayin bincike, mutanen sun bayyana cewa suna kan hanyarsu daga Birnin Gwari zuwa wurare daban-daban, kwatsam maharan suka tarbe su.
Kakakin NAF ya ƙara da cewa a halin yanzun dakarun SF sun ƙara matsa kaimi a yankin da nufin ceto sauran matafiyan da aka sace.
A cewarsa, waɗan aka ceto a halin yanzu, sojojin sun kai su Asibitin rundunar sojin NAF dake Kaduna domin duba lafiyarsu.
A wani labarin kuma Yan bindiga sun halaka mutum sama da 30, sun kona kauyuka a jihar Neja
Miyagun yan bindiga sun kona gidajen mutane baki ɗaya a wani mummunan hari da suka kai kauyuka biyu a jihar Neja.
Wani da aka kashe mutum 10 daga iyalansa, ya bayyana cewa zuwa yanzun sun sake gano wasu gawarwaki na daban 20 a cikin jeji.
Asali: Legit.ng