Shugaba Buhari ya aike da tawagar wakilai Zamfara kan kashe mutane 200
- Wakilan gwamnatin shugaba Buhari sun dira Gusau, babban birnin Zamfara domin jajantawa gwamnati kan harin kwanan nan
- Tawagar FG taje Gusau ne bisa jagorancin ministan tsaro, Bashir Magashi, da ministan ayyukan jin ƙai, Sadiya Umar Farouq
- Awanni kaɗan da suka gabata, gwamnonin APC suka ziyarci Matawalle a fadar gwanatinsa domin jajanta masa kan harin
Zamfara - Wakilan gwamnatin tarayya sun dira Gusau, babban birnin jihar Zamfara, ranar Laraba, domin jajantawa gwamnatin jihar bisa harin yan bindiga na kwanan nan.
Punch ta rahoto cewa tawagar wakilan karkashin jagorancin Ministan tsaro, Bashir Magashi, ta kunshi, ministan ayyukan jin kai, Sadiya Umar Farouq, da kakakin Buhari, Malam Garba Shehu.
Sauran mambobin tawagar sun haɗa da, ministan harkokin yan sanda, Muhammad Dingyadi, mai bada shawara kan tsaro, Babagana Monguno, da kuma Sufeta janar na yan sanda, Usman Baba.
Wane hari suka je jajantawa?
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda wasu tsagerun yan bindiga suka kai mummunan hari kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
An samu banbancin adadin mutanen da aka kashe yayin harin, amma gwamnatin Zamfara tace mutanen da aka kashe sun wuce 50.
Amma wasu majiyoyi sun bayyana cea maharan sun halaka mutane kusan 200 yayin mummunan harin, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Gwamnonin APC sun je jaje
Kazalika, gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki, sun ziyarci takwaransu na Zamfara, Bello Matawalle, awanni kaɗan da suka shuɗe domin jajanta masa kan lamarin.
Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, sun kai ziyara jihar domin jajantawa al'umma.
Gwamna Bagudu na jihar Kebbi, ya roki a ƙara danƙon haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da ta tarayya domin magance wannan matsalar da ta zama barazana ga ƙasa.
Yace duk da gwamnati ta yi kokari sosai wajen magance rashin tsaro, amma akwai bukatar ƙara zage dantse da bin duk wasu hanyoyin kawo karshen ta'addanci.
A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023
Jam'iyyar APC ta nuna goyon bayanta 100 bisa 100 kan takarar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a zaben 2023.
Shugaban APC reshen jihar Ebonyi, Mista Emegha, yace matukar gwamnansa ya zama shugaban ƙasa, to Najeriya zata yi gogayya da sauran ƙasashe.
Asali: Legit.ng