Yanzu-Yanzu: Tsohon gwamna, kuma jigon APC a Oyo ya riga mu gidan gaskiya
- Rahoton da ke fitowa daga majiyoyi ya bayyana cewa, tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Adebayo Alao-Akala ya riga mu gidan gaskiya
- Rahotanni sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar yau Laraba, 12 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2022
- Ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, domin majiya bata bayyana jawabi daga danginsa ba
Ogbomoso, Oyo - Wani tsohon gwamnan jihar Oyo, Otunba Adebayo Alao-Akala, ya rasu da sanyin safiyar Laraba a Igbomoso.
Akala, jigo a jam’iyyar APC, ya kasance tsohon gwamnan jihar, tsakanin 2007 zuwa 2011, Vanguard ta rahoto.
Ya kuma kasance mataimakin gwamna a karkashin tsohon gwamna, Rashidi Ladoja tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006, lokacin da aka tsige Cif Ladoja, wanda a sakamakon haka ya zama gwamnan rikon kwarya na tsawon watanni goma sha daya.
Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya tabbatar da mutuwar magabacin nasa Otunba Adebayo Alao-Akala.
Makinde ya bayyana haka ne a lokacin da aka kira shi da ya yi jawabin fatan alheri a ci gaba da gudanar da addu’o’in mabiya addinai na ma’aikatan Oyo.
Gwamnan ya ce ya samu labarin ne yayin da yake cikin taron, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu
A wani labarin, Cif Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya wacce ta gaji mulkin Janar Ibrahim Babangida, ya rasu.
Shonekan ya rasu a jihar Legas yana da shekaru 85 a duniya, kamar yadda The Guardian ta rahoto.
Ya kasance shugaban kasa Najeriya na wucin gadi tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba, 1993 lokacin da aka hambarar da shi a juyin mulkin da marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranta.
Asali: Legit.ng