Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki gari a Katsina, sun sanya harajin N10,000 kan kowa
- Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari wani yankin Katsina, sun saka wa jama'a harajin N10,000 a yankin
- Rahotanni sun ce, an kai harin a wani yankin da ake sarrafa gwal, inda aka sace wasu mutane da yawa a wurin
- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce tana nan tana ci gaba da bincike
Katsina - ’Yan bindiga sun sanya harajin Naira 10,000 a wani yankin sarrafa gwal da ke karamar hukumar Jibia a Jihar Katsina, domin ci gaba da hako ba tare da tasgaro ba.
Wurin yana cikin al'ummar Bakin Korama a garin Magama Jibia kan iyakar yankin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa akalla kananan cibiyoyin sarrafa gwal 70 ne ke gudanar da aiki a wurin, wanda aka bude kimanin makwanni biyu da suka gabata.
An gano cewa ‘yan bindigan sun dorawa ma’aikatan harajin ne bayan sun mamaye wurin a daren ranar Alhamis inda suka kashe biyu daga cikin ma’aikatan.
A cewar mazauna garin, harin ya fara ne da misalin karfe 8 na dare kuma ya dauki tsawon sa’o’i biyu ana barna, inji rahoton Punch.
An kuma ce wasu ma’aikata biyar sun jikkata a harin, yayin da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da ma’aikata 11 a wurin.
Shugaban masu sarrafa gwal ya magantu
Shugaban masu sarrafa ma’adanai ta Katsina Tasi’u Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa daga baya ‘yan bindigan sun sako daya daga cikin ma’aikatan da aka yi garkuwa da su, wanda suka umurta da ya kai wasikar da ke nuna dora musu harajin.
Abdullahi ta bayyana cewa:
“A ranar Alhamis, ‘yan bindiga sun kai hari da misalin karfe 8:10 na dare. Sun zo ta wani kogi da ke makwabtaka da nan. Da isar su sai suka fara karbar kudi daga hannun mutanen bayan wani yaro ya sanar da mutane zuwan su da ihun ‘yan bindiga, ‘yan bindiga."
Abdullahi ya kara da cewa, a shirye suke su bi duk wani shirin da gwamnati za ta yi na kare rayuwarsu da kasuwancinsu, don haka ba za su kulla yarjejeniya da ‘yan bindiga ba.
Leadership ta tattaro cewa masana’antar gwal na yankin na kewaye da ’yan kasuwa, inda yara, mata da manyan maza ke sayar da abinci, abin sha, da tufafi da dai sauransu.
Haka kuma akwai jami'an tsaro a wurare masu mahimmanci na masana'antar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.
A wani labarin, Wani mummunan lamari ya faru a wani kauye da ke cikin jihar Katsina – inda nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fito.
Rahoton da jaridar Katsina Post ta fitar a ranar Talata, 11 ga watan Junairu, 2022, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun dauke wata mata mai shayarwa.
Miyagun ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da wannan mai jego mai suna Malama Saratu da kuma ‘diyar da take shayarwa a ranar Litinin cikin dare.
Asali: Legit.ng